Home Back

Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Gwamna Ya Naɗa Sabon Sarki Mai Martaba

legit.ng 2024/7/1
  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da naɗin Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin ƙasar Ibadan atau Olubadan
  • Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon Olubadan, Oɓa Balogun, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa ranar 14 ga watan Maris, 2024
  • A wurin taron da gwamnatinsa ta shirya, Makinde ya ce ya ga sakon majalisar naɗa sarki kuma ya amince da wanda masu naɗa sarki suka zaɓa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ta bayyana cewa ya amince da naɗin of Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin Ibadanland watau Olubadan.

Makinde ya amince da naɗin sabon sarkin mai daraja biyo bayan shawarin da ya karɓa daga majalisar masarautar.

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamna Makinde ya amince da nadin sabon Olubadan na Ibadanland a jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde Asali: Facebook

Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taro na musamman da gwamnatin Oyo ta shirya na bankwana da marigayi Olubadan, Oba Olalekan Balogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Leadership ta tattaro, Balogun ya rasu ne ranar 14 ga watan Maris, 2024 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Gwamna Makinde ya ce ya ga shawarwarin da majalisar masu naɗin sarkin suka aiko masa kuma ya amince da su.

"Na yarda da hakan kuma da zaran Olubadan mai jiran gado, Oba Owolabi Olakulehin, yana da ƙoshin lafiya za a naɗa shi a karagar mulki tun da an bi ƙa'ida," in ji shi.

Makindw ya ce marigayi Olubadan ya yi rayuwa mai gamsarwa, inda ya ƙara da cewa shi da marigayi sun yi abubuwan da mutane da yawa ke tunanin ba za su taba yiwuwa ba.

"Ni da Oba Balogun mun gayara dokar naɗin sarauta a Ibadan wanda ya haɗa har da naɗin Oƙubadan."

Tsohon babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Lt.-Gen. Tukur Yusuf Buratai (rtd), ya bayyana Balogun a matsayin mutumin kirki mai son taimakon jama’a.

Buratai ya ƙara da cewa Marigayi Balogun ya yi wa jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya hidima, ya taimakawa al'umma da hanya daban-daban.

Bola Tinubu ya yabawa Makinde

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan su yi koyi da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta ya ce jikoki masu tasowa ba zasu manta da Gwamna Makinde ba

Asali: Legit.ng

People are also reading