Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Gwamna Ya Naɗa Sabon Sarki Mai Martaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ta bayyana cewa ya amince da naɗin of Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin Ibadanland watau Olubadan.
Makinde ya amince da naɗin sabon sarkin mai daraja biyo bayan shawarin da ya karɓa daga majalisar masarautar.
Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taro na musamman da gwamnatin Oyo ta shirya na bankwana da marigayi Olubadan, Oba Olalekan Balogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Leadership ta tattaro, Balogun ya rasu ne ranar 14 ga watan Maris, 2024 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Gwamna Makinde ya ce ya ga shawarwarin da majalisar masu naɗin sarkin suka aiko masa kuma ya amince da su.
"Na yarda da hakan kuma da zaran Olubadan mai jiran gado, Oba Owolabi Olakulehin, yana da ƙoshin lafiya za a naɗa shi a karagar mulki tun da an bi ƙa'ida," in ji shi.
Makindw ya ce marigayi Olubadan ya yi rayuwa mai gamsarwa, inda ya ƙara da cewa shi da marigayi sun yi abubuwan da mutane da yawa ke tunanin ba za su taba yiwuwa ba.
"Ni da Oba Balogun mun gayara dokar naɗin sarauta a Ibadan wanda ya haɗa har da naɗin Oƙubadan."
Tsohon babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Lt.-Gen. Tukur Yusuf Buratai (rtd), ya bayyana Balogun a matsayin mutumin kirki mai son taimakon jama’a.
Buratai ya ƙara da cewa Marigayi Balogun ya yi wa jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya hidima, ya taimakawa al'umma da hanya daban-daban.
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan su yi koyi da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta ya ce jikoki masu tasowa ba zasu manta da Gwamna Makinde ba
Asali: Legit.ng