Home Back

Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Ƙaru da Naira Tiriliyan 24 a Cikin Wata 3 Kacal, Rahoton DMO

legit.ng 2024/7/3
  • Ofishin kula da basussuka (DMO) ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai zuwa Naira tiriliyan 121.67 cikin watanni uku
  • Rahoton DMO ya nuna cewa gwamnatin Tinubu ta karbo rancen Naira tiriliyan 6.53 tsakanin watan Disambar 2023 zuwa Maris 2024
  • Basusukan da ake bin Nijeriya ya ƙunshi bashin cikin gida da na waje da gwamnatin tarayya, jihohi gami da FCT, Abuja suka karbo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Adadin bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya kai Naira tiriliyan 121.67 (dala biliyan 91.46), in ji ofishin kula da basussuka (DMO) a ranar Alhamis.

Bayanan da DMO ta fitar sun nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta karbo rancen kudi har Naira tiriliyan 6.53 tsakanin watan Disamba zuwa Maris.

Hukumar DMO ta yi magana kan bashin da ake bin Najeriya
Ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 121.67, in ji rahoton hukumar DMO. Hoto: Getty Images, officialABAT/X. Asali: Getty Images

Hukumar ta DMO ta ce ya zuwa ranar 31 ga Maris, 2024, basussukan cikin gida da na waje na kasar sun tsaya a kan Naira tiriliyan 121.67 (dala biliyan 91.46).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana bin Najeriya bashin N121.67tr

Bashin Najeriya ya karu da Naira tiriliyan 24.33 a cikin watanni uku - daga Naira tiriliyan 97.34a watan Disambar 2023 zuwa Naira tiriliyan 121.67, in ji rahoton Channels TV.

Bashin yana wakiltar rancen waje da na cikin gida da gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya (FCT) ke karbowa.

Yayin da aka saka jimillar bashin cikin gida a kan Naira tiriliyan 65.65 (dala biliyan 46.29), jimillar bashin na waje ya kai Naira tiriliyan 56.02 (dala biliyan 42.12).

Jaridar The Cable ta ruwaito DMO ta bayyana cewa jimillar basussukan jama'a ya karu daga Naira tiriliyan 59.12 a watan Disambar 2023 zuwa Naira tiriliyan 65.65 a Maris din 2024.

Dalilin karuwar bashin da ake bin Najeriya

An rage yawan basussukan a kudin Amurka da dala biliyan 16.77 kwatankwacin kashi 18.34, domin karuwar bashin ya faru ne biyo bayan faduwar darajar da Naira ta yi.

Ofishin ya yi amfani da canjin kudi na N1,330/1$ wajen auna kimar basussukan waje daga N899.39 da canja dala a watan Disambar 2023 wajen auna kimar bashin.

An kuma alakanta karuwar bashin da wani sabon rance da Shugaba Tinubu ya yi domin cike wani bangare na gibin kasafin kudin shekarar 2024.

Akwai kuma bashin Naira tiriliyan 7.3 da Najeriya ta samu daga babban bankin Najeriya da kuma sama da dala biliyan 2.2 daga wajen bankin duniya.

Najeriya za ta karbo sabon bashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta garzaya Bankin Duniya inda ta ke neman rancen dala miliyan 500 domin gina tituna a karkara.

Wannan na zuwa ne bayan da Bankin Duniya ya amince zai ba Najeriya tallafin bashin dala biliyan 2.25 domin bunkasa tattalin arzikinta.

Asali: Legit.ng

People are also reading