Home Back

AMBALIYA, TA’ADDANCI: Muna neman ɗauki daga gwamnatin tarayya Kogi – Gwamna Ododo na Kogi

premiumtimesng.com 2024/5/20
AMBALIYA, TA’ADDANCI: Muna neman ɗauki daga gwamnatin tarayya Kogi – Gwamna Ododo na Kogi

Gwamnan jihar Kogi Usman Ododo ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kawo wa jihar Kogi dauki kan ambaliya da ke neman tunkaro ji har a yanzu.

Ododo ya fadi haka ne yayin da tawagar hukumar RMAFC suka kawo masa ziyarar a fadar gwamnatin jihar dake Lokoja ranar Asabar.

Ya ce jihar Kogi ita ce mahaɗar matafiya daga yankin Kudu zuwa Arewa haka kuma daga yankin Arewa zuwa Kudu.

Gwamna Ododo ya ce idan ba a maida hankali an kawar da wannan matsala ba, zai iya shafar jihohin da ke makwabtaka da jihar Kogin.

“A dalilin haka ya sa muke rokon gwamnati da ta kawo mana dauki a wannan jihar tamu.

Shugaban tawagar Bako Shettima ya yi alkawarin duba batutuwan da aka gabatar wa hukumar domin magance su.

Bayan haka sai gwamna Ododo ya garzaya da tawagar zuwa duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ta aiwatar zuwa yanzu.

People are also reading