A Karshe, Tinubu Ya Fadi Mafi Karancin Albashi da Zai Iya Biya, NLC Ta Bukaci N250,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa kan mafi karancin albashi da za ta iya biya.
Bayan doguwar ganawa da aka yi, a karshe Bola Tinubu ya bayyana N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatin za ta biya.
Wannan na zuwa ne bayan N60,000 da ta ce za ta biya a baya wanda kungiyar kwadago ya NLC ta ki amincewa da shi, cewar Channels TV.
Har ila yau, kungiyar NLC na neman N250,000 bayan ta sauko daga N494,000 da ta bukata tun farko.
Karin bayani na tafe....
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng