Home Back

Kotu Ta Dauki Mataki Kan DSTV da GOtv, Ta Umarci Ba Ƴan Najeriya Damar Kallo Kyauta

legit.ng 2024/7/7
  • Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta dauki mataki kan kamfanin Multichoice na DSTV da GOtv bayan kara kudi ga kwastomomi
  • Kotu ta ci tarar kamfanin N150m tare da umartarsa da ya ba ƴan Najeriya damar kallo ba tare da biya ba har tsawon wata daya
  • Wannan na zuwa ne bayan kamfanin ya kara kuɗin da ake biya kafin kallon tashoshinsa wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun sauraran kararraki da koken kwastomomi ta ci tarar kamfanin Multichoice da ke da DSTV da GOtv N150m.

Kotun ta kuma umarci kamfanon ya ba ƴan Najeriya damar kallon tashoshinsa kyauta na tsawon wata daya.

Kotu ta ci tarar DSTV da GOtv N150m kan kara kudin tashoshi
Kotu ta ci tarar DSTV da GOtv N150m bayan kara kudin tashoshi ba bisa ka'ida ba. Hoto: Pius Utomi Ukpei. Asali: Getty Images

Karin kudi: Matakin kotu kan DSTV, GOtv

Mai Shari'a, Thomas Okosu wanda ya jagoranci kwamitin alkalai uku shi ya yanke wannan hukuncin bayan wani lauya ya maka kamfanin a kotu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan mai suna Festus Onifade shi ya maka kamfanin a kotu bayan kara kudin da suka yi wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Mayu.

Har ila yau, kotun ya dakatar da Multichoice daga karin kudin ga kwastomominsa inda ta ce hakan saba doka ne.

Hukumar FCCPC ta zargi kamfanin da kara kudin ba tare da sanar da kwastomominsa wata daya kafin sanarwar ba.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading