Home Back

Ya Kamata A Karfafa Manufar Amfani Da Harsunan Gado A Makarantu

leadership.ng 2024/6/30
Ya Kamata A Karfafa Manufar Amfani Da Harsunan Gado A Makarantu

Shekaru biyu bayan gwamnatin tarayya ta bayyana manufar harshen da ya kamata a rika koyarwa da shi a makarantu, ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba wajen aiwatar da shirin. Makarantu da yawa har yanzu suna amfani da Ingilishi a matsayin harshen koyarwa, kuma an ci gaba da koyar da harsunanmu na gado a matsayin darussa na daban. A wasu makarantun ma,ba su dauki koyar da harsunanmu na gado da muhimmanci ba.

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da manufar Harsuna ta Kasa (NLP) a shekarar 2022, wanda ya sa harsunan gado suka zama tilas a rika amfani da su wajen koyarwa tun daga aji daya zuwa aji shida na makarantar Firamare.

Shekaru biyar kafin amincewar majalisar zartarwar, a shekarar 2017, gwamnatin tarayya ta bayyana wani shiri na makarantun Firamare da Sakandare na Nijeriya da za a rika koyar da darussan lissafi da kimiyya a cikin harsunan asali. Daga nan sai gwamnati ta kafa kwamitin ma’aikatu da suka hada da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta tarayya da ma’aikatar ilimi ta tarayya da za su tabbatar da nasarar shirin.

Ana sa ran kwamitin ya samar da wani shiri na bunkasa amfani da harsunan gida da samar da ingantattun kayan aiki don koyar da ilimin lissafi da darussan kimiyya da kyau. Hanya ce da kasashe irin su Sin da Indiya suka dauki shekaru da dama suna amfani da ita a baya, lokacin da suka rungumi dabarun da suka dace da kasashensu da yanayin al’ummominsu ta hanyar koyar da ilmin lissafi da darussan kimiyya a cikin harsunansu na asali a matakin firamare.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta jaddada cewa za a iya aiwatar da manufofin gaba daya ne kawai idan aka samar da kayan koyarwa da kuma samar da kwararrun malamai, amma da alama ba a yi wani abu na cimma hakan ba bayan shekara biyu.

A kwanan nan, Cibiyar Bunkasa Ci gaban Harshe (LDC) ta ce an fara aiwatarwa amma har yanzu abin yana kan matakin farko. Bayanai sun nuna cewa gwamnati tana kokarin magance kalubalen da ke zama karfen kafa ga shirin kafin manufar ta fara aiki a fadin kasa baki daya. Amma kuma, duk da haka, ba a gani a kasa ba. Kenan a ina gizo yake sakar?

Daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da tafiyar hawainiya a wannan ci gaba na shi ne rashin horar da malamai wadanda za su iya koyar da harsunan gado yadda ya kamata. Dole ne gwamnati ta zuba jari mai yawa a cikin shirye-shiryen horar da malamai don tabbatar da cewa malamai sun sami kwarewar da ta dace don koyar da wadannan harsuna.

Wani kalubale kuma ga samun nasarar shirin shi ne rashin daidaitattun kayan koyarwa a cikin harsunan gado. A ra’ayinmu, dole ne gwamnati ta yi aiki tare da masu buga littattafai don habaka littattafan karatu da sauran kayan aiki na kayan koyarwa a cikin wadannan harsuna. Wannan ba wai kawai zai taimaka wa dalibai su koyi karatu da kyau ba ne, amma kuma zai taimaka wajen adanawa da habaka wadannan harsuna.

Bugu da kari, ya dace a ce manufar ta kunshi litattafai a cikin wadannan harsuna, wadanda za a samar da su domin koyar da ilmin lissafi da kimiyya da horar da malaman da a yanzu za su yi amfani da harsunan wajen koyar da yara a makarantun firamare da sakandare.

A ra’ayinmu, ya kamata gwamnati ta horar da kuma daukar malaman da suka kware wajen amfani da harsunan gida aikin koyarwa a makarantu. Hakan zai tabbatar da cewa ana koyar da dalibai a cikin yarensu na asali kuma za su iya fahimtar darussan da ake koyar da su sosai.

Manufofin harshe da tsarin ilimin ya dauka, babu shakka yana daya daga cikin mafi karfi a cikin salo daban-daban da ake amfani da su wajen sarrafa harshe. Bayan cibiyoyin addini, makaranta ita ce mafi kusa da tsarin amfani da harshen gida. A hakika, yawancin yara suna samun gibi mai yawa a tsakanin yarensu na asali (wanda aka fi sani da yare ko harshen gado) da kuma yaren da ake amfani da shi a makaranta, wanda galibi ana amfani da shi ne a matsayin harshen kasa ko kuma na hukuma.

Amfani da harsunan asali a makarantu yana da fa’idodi da yawa. Yana bai wa dalibai damar koyo cikin harshensu na asali, inganta aiki da ilimin da aka koya da kuma haifar da mafi kyawun sakamako da riko da abin da aka koya. Har ila yau, yana taimakawa wajen adanawa da habaka wadannan harsuna, wanda yake zama wani muhimmin sashi na al’adun Nijeriya. Ana kuma sa ran manufar za ta inganta da kuma kiyaye harsunan Nijeriya.

Haka kuma, koyar da darussan kimiyya da zamantakewa a cikin harsunan asali na iya taimakawa wajen cike gibin da ke tsakanin ilimin da aka gada iyaye da kakanni da kimiyyar zamani. Harsuna na asali galibi suna da kalmomi da ra’ayoyin da babu su cikin Ingilishi,kuma koyarwa a cikin wadannan harsunan na iya taimakawa wajen habaka wannan ilimin a cikin manhajar karatuttuka.

Ya kamata gwamnati ta sanya ido tare da tantance yadda ake aiwatar da manufofin harshe don tabbatar da yin tasiri tare da cimma nasarar da abubuwan da ta kunsa.

+.3Wannan zai taimaka wajen gano wuraren da za a inganta da yin gyare-gyaren da suka dace da manufofin.

Wannan yana nufin cewa domin manufar ta samu nasara, dole ne gwamnati ta zuba jari mai yawa don horar da malamai tare da samar da daidaitattun kayan koyarwa a cikin wadannan harsuna.Ta yin haka, Nijeriya za ta iya taimakawa wajen adanawa da habaka al’adunta tare da inganta ingancin ilimin dalibanta.

A gaskiya, a ra’ayin wannan jaridar, ya kamata gwamnati ta samar da cikakken tsarin manufofin harshe wadanda ke bayyana makasudi, dabaru, da ka’idoji da za a yi amfani da su wajen aiwatar da amfani da harsunan gida a matsayin harshen koyarwa a makarantu.

People are also reading