Home Back

‘Wanda ya ce na kamfaci Dala 720,000 na Kogi na biya kuɗin makarantar ɗa na, maƙaryaci ne’- Yahaya Bello

premiumtimesng.com 2024/5/17
‘Wanda ya ce na kamfaci Dala 720,000 na Kogi na biya kuɗin makarantar ɗa na, maƙaryaci ne’- Yahaya Bello

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya ƙaryata zargin da Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya yi masa cewa ya daga cikin Naira biliyan 80 ɗin da ya sata daga Jihar Kogi, ya kamfaci Dala 720,000 ya biya kuɗin makarantar ɗan sa ɗaya tal da ke karatu a wata American School, a Abuja.

Ita ma makarantar da ake magana, ta fitar da wasu kwafen takardun da ke nuna cewa ta maida wa Yahaya Bello Dala 720,000 ɗin da ya biya don karatun yaron na sa.

Takardar wadda aka fitar ranar Juma’a, ta nuna Yahaya Bello ya kuɗin a cikin watan Agusta, 2021, a matsayin somin-taɓin fara biyan kuɗin makarantar yaron.

Wasiƙar na ɗaya daga cikin hujjoji da EFCC ta dafe a hannun ta, wadda za ta gabatar wa kotu kan taɓargazar da Yahaya Bello ya yi, lokacin ya na gwamnan Kogi.

To sai dai kuma Yahaya Bello wanda ya kammala wa’adin mulki cikin Janairu, 2023, ya ce ‘ya’yan sa sun fara karatu a American School tun ma kafin ya zama gwamna cikin 2016.

Sai dai kuma Ofishin Yaɗa Labaran Yahaya Bello ya ce dukkan kwafen takardun da EFCC ke watsawa a soshiyal midiya, ba na gaskiya ba ne ƙoƙarin keta wa Bello haddi hukumar ke yi ba bisa ƙa’idar bin doka ba.

Saboda haka ofishin ya ce duk wani sharri da ƙage ba zai yi tasiri kan Yahaya Bello ba.

People are also reading