Home Back

Bayan Kwace Kadarorin N12bn, Tsohon Gwamnan CBN Ya Nemi Alfarma a Kotu

legit.ng 2024/7/5
  • Godwin Emefiele ya buƙaci babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba shi izinin zuwa ganin likita a ƙasar waje
  • Tsohon gwamnan ya shigar da wannan buƙata ne ta hannun lauyansa, Mathew Burkaa kuma har yanzun mai ƙara watau EFCC ba ta ce komai ba
  • Emefiele na ci gaba da fuskantar shari'a kan tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa bayan shugaban ƙasa ya sauke shi daga gwamnan CBN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya buƙaci babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba shi izinin fita ƙasar waje.

Mista Emefiele ya nemi izinin tafiya waje domin a duba lafiyarsa a gaban kotun da yake fuskar shari'a kan tuhume-tuhumen satar kuɗin baitul-mali.

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Godwin Emefiele ya nemi izinin fita ƙasar wajen domin duba lafiyarsa Hoto: Mr.Godwin Emefiele Asali: Twitter

Lauyan tsohon gwamnan CBN, Mathew Burkaa ne ya tunatar da alƙalin kotun game da wannan buƙata a zaman ranar Talata, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai lauyan bai yi cikakken bayani kan rashin lafiyar da ke damun Emefiele ba da har ta kai ga yake neman izinin tafiya ƙasar waje.

Idan baku manta ba Alkalin kotun, Hamza Mu’azu, ya bayar da umarnin a kwace fasfo din Mista Emefiele a wani bangare na sharudɗan belinsa.

Don haka ne tsohon gwamnan ya nemi a ba shi fasfo ɗinsa domin ya tafi ganin likitansa a ƙasar waje.

Mai shari'a Mu'azu ya sanya ranar 8 ga watan Yuli, 2024 domin sauraron buƙatar wanda ake ƙara da kuma yiwuwar yanke hukunci, rahoton Ripples Nigeria.

Har kawo yanzu, hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ba ta ce komai ba game da buƙatar Emefiele.

A shari’ar, EFCC na tuhumar Emefiele da laifuka 20 da suka hada da buɗe ƙofar cin hanci da rashawa, hada baki, zagon kasa, ƙarya, da kuma karbar kusan $6.23m ba bisa ka'ida ba.

Tun da Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga kujerar gwamnan CBN a watan Yuni, Emefiele ke fuskantar shari'a kan tuhumar almundahana a Abuja da Legas.

EFCC ta bankaɗo rabon kwangila a CBN

A wani rahoton kun ji cewa hukumar EFCC ta shaidawa kotu zargin da ta ke na yadda tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele ya yi watandar kwangila.

Shaidan EFCC na bakwai ya ce tsohon shugaban babban bankin kasa, Mista Emefiele ya raba kwangiloli ga mai dakinsa da dan uwanta a zamaninsa.

Asali: Legit.ng

People are also reading