Atiku Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Sa Aka Gaza Gyara Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta azabtar da yan Najeriya cikin shekara daya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Atiku Abubakar na cewa mulkin Tinubu ya zama kamar bulaliyar kan hanya wacce bata bar talaka da mai kudi ba.
Ya kuma kara da cewa tsare-tsare masu tsauri da Bola Tinubu ya kawo sun kori masu zuba jari da dama daga ƙasashen ketare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Atiku Abubakar ya ce tsare-tsaren da Tinubu ya bullo dasu musamman a harkokin tattalin arziki sun nakasa yan kasuwa a kasar.
A cewarsa, hakan yasa talakawan na kara shiga kangin talauci masu kuɗi kuma na talaucewa a faɗin kasar, rahoton Leadership.
Atiku Abubakar ya kara da cewa an samu tashin farashin kayyakki mafi muni a tarihin Najeriya a mulkin Bola Tinubu.
Ya ce a watan Afrilu an samu tashin kayan abinci da kashi 40.53% wanda shi ne mafi muni a shekaru 15 da suka wuce.
Atiku Abubakar ya ce kamfanoni irinsu Unilever, Bolt Food, Equinor da sauransu duk sun fice daga Najeriya saboda tsauraran matakan da gwamnatin ta dauka.
Ya ce hukuma NECA ta bayyana cewa sama da kamfanoni 15 suka fice daga Najeriya wanda yasa an rasa ayyuka kimanin 20,000.
A karshe Atiku Abubakar ya ce matuƙar ana son fitar da Najeriya daga halin da take ciki dole sai Bola Tinubu ya saka tausayi cikin mulki wajen rage tsauraran matakan da ya dauka.
A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya yi karin haske kan maganar hadakarsa da Atiku Abubakar
Peter Obi ya ce matuƙar aka samu daidaito kan yadda za a magance matsalolin Najeriya a tsakaninsu zai goyi bayan haɗakar dari bisa dari.
Asali: Legit.ng