Home Back

Yan Sanda a Legas sun Damke Fasinjan da ya yi Yunkurin Kwacen Mota

legit.ng 2024/7/3
  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta bayyana cafke wani mutum mai shekaru 35 da ya yi yunkurin sace tasin da ya hawo daga Chevron dake Ajah zuwa gidan boka a Agidigbi a Alausa
  • A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, wanda aka yi yunkurin yiwa satar ne ya mika kokensa ga ofishinsu dake yankin Alausa, inda jami’ai suka bi sawun barawon
  • Tun da fari dai matashin ya zare wuka ne tare da tsorata mai tasin, amma ya jajirce su ka fara kokawa har ya ji masa rauni, daga nan kuma ya cika wandonsa da iska

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da kama wani matashi mai shekaru 35 bayan ya yi yunkurin kwace tasin da ya hau a hanyar filin jirgin saman jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin da ya tabbatar da kama matashin wanda aka yi yunkurin yiwa satar ne ya shigar da korafi ofishinsu dake Alausa.

Police
Amma kama matashin da ya yi yunkurin satar tasi a Legas Hoto: Lagos State Police Command Asali: Facebook

A sakon da rundunar ta wallafa a shafinta na X, jami’an yan sanda sun bayyana cewa sai da aka yi gudun ‘yan tsere da barawon kafin a kai ga cafke shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ‘yan sanda su ka kama matashin

Rundunar ‘yan sandan Legas ta bayyana cewa wani matashi ya yanki mai tasi a kokarin yi masa satar tasin da ya ke samun abin kaiwa bakinsa a jihar Legas.

Vanguard News ta wallafa cewa tun da fari, fasinjan ya tsayar da mai tasi a yankin Chevron da ke Ajah , inda ya nemi a kai shi gidan boka a Agidigbi a Alausa da ke Ikeja.

Amma bayan sun isa wuraren bankin Mobolaji ne fasinjan ya yi fito da wuka ya kuma yi kokarin kwace masa mota, a nan ne su ka yi kokawa har aka yanki mai tasin.

Daga nan mai tasin ya yi kururuwai neman dauki kuma jama’a suka fito tare da bin barawona guje har aka kai ga kama shi bayan gudu mai nisa.

An kama buhun wuri 30 a Legas

A wani labarin kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta yi nasarar cafke wani mutum dauke da buhunhunan wiwi guda 30 a yankin Ojo da sanyin safiyar ranar Laraba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatarwa manema labarai kamen tare da bayar da tabbacin zurfafa bincike domin gano sauran wadanda ake harkar da su.

Asali: Legit.ng

People are also reading