Home Back

Tinubu Ya Bi Sahun Atiku Kan Ta'aziyyar Kisan Katsina, Ya Ba Jami'an Tsaro Sabon Umarni

legit.ng 2024/6/28
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana da kakkausar murya kan hare-haren da ƴan bindiga suka kai a wasu ƙananan hukumomin jihar Katsina
  • Shugaba Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su zaƙulo ƴan bindigan da suka kai hare-haren a ƙananan hukumomin Dutsinma da Kankara
  • Ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, gwamnati da al'ummar jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kakkausar suka kan kashe-kashen da ƴan bindiga suka yi a jihar Katsina.

Ƴan bindigan dai sun kai hare-hare cikin ƴan kwanakin nan a ƙananan hukumomin Dutsinma da Kankara na jihar Katsina.

Tinubu ya yi Allah wadai kan kashe-kashe a Kaduna
Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu a hare-haren Katsina Hoto: @DOlusegun Asali: Facebook

Ƴan bindigan a yayin hare-haren sun hallaka rayukan mutane da dama waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan hare-haren Katsina?

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su zaƙulo ƴan bindigan da suka kai hare-haren a ƙananan hukumomin Dutsinma da Kankara.

Ya kuma umarci su tabbatar da cewa waɗanda suka kai hare-haren an yi musu hukuncin da ya dace.

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

Shugaba Tinubu wanda ya yi kakkausar suka kan sababbin hare-haren da ake kaiwa a yankunan, ya bayyana su a matsayin waɗanda suka ƙazanta.

Shugaba Tinubu,ya jaddada cewa za a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron ƴan ƙasa da kuma kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta’adda gaba ɗaya da sauran masu tayar da ƙayar baya a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, gwamnati da al’ummar jihar Katsina, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu.

Atiku ya yi Allah wadai da kisan Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda aka mayar da ran ƴan ƙasar nan ba a bakin komai ba.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan wanda ya yi Allah wadai da kisan da ƴan bindiga suka yi a jihar Katsina, ya koka kan yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Asali: Legit.ng

People are also reading