Home Back

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Haramar Sayowa Tinubu da Shettima Jirgin Sama a Kasar Waje

legit.ng 2 days ago
  • Bayanai sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta na kokarin sayo jirgin saman da fadar shugaban kasa za ta rika amfani da shi
  • Gwamnatin Najeriya za ta sayo jirgin saman ne a lokacin da jama’a su ke kuka kan tsadar rayuwa da farashin kayan abinci
  • Masu mulki kuma suna kukan jiragen fadar shugaban kasa sun samu matsala don haka ana bukatar nemowa Bola Tinubu jirgi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Idan abubuwa suka tafi a yadda ake tunani yanzu, gwamnatin Najeriya za ta sayo jirgin sama domin zirga-zirgar fadar shugaban kasa.

Jami’an fadar shugaban kasa sun yi gum game da batun bayan an koka cewa jiragen fadar shugaban kasa sun samu matsala, an sa su a kasuwa.

Jirgin fadar shugaban kasa
Gwamnatin Najeriya za ta sayowa jirgin fadar shugaban kasa Hoto: @NgrPresident/aircraft.airbus.com Asali: UGC

Wani kebantaccen rahoton Premium Times ya ce ana kokarin sayen jirgin saman Airbus A330 a hannun wani attajirin balarabe a kasar waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan balarabe wanda ‘dan kasuwa ne kuma basarake ya shiga matsalar kudi ne, har ya gaza biyan bashin banki da ya karba a kasar Jamus.

Najeriya za ta samu jirgin sama a bagas?

Ana zargin ‘dan kasuwar ya yi amfani da jirgin wajen cin bashi a bankin kasar Jamus, yanzu da ya gagara biyan kudin, sai aka saida kadararsa.

Daily Trust ta ce da farko bankin ya rike jirgin da aka ba da a matsayin jingina, amma ganin irin kirarsa, sa ake neman saida shi a kasuwa.

Idan lamarin ya tabbata, a yanzu jirgin saman yana hannun kamfanin L & L International LLC na Amurka wanda ake so ya saidawa Najeriya.

Za a samu jirgin saman da araha?

Idan gwamnatin Najeriya ta saye jirgin, wasu wadanda suka san harkar jiragen sama sun ce za ta iya cin riba idan aka yi nufin saida shi a kasuwa.

Da aka tambayi kamfanin, sun ki cewa komai a game da zancen, amma ana tunanin gwamnatin ta na nemo kudin da za ta saye jirgin ne.

Watakila a iya saidawa gwamnati jirgin na Airbus a kan N180bn, babu mamaki a fito da kudin daga kason SWV da aka yi a cikin kasafin kudin 2023.

Bola Tinubu ya ba Radda mukami

Shekara guda da darewa kan karagar mulki sai aka ji labari shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba Gwamna Dikko Umar Radda mukami a NDPHC.

Shugaban kasa ya dauko gwamnan jihar Katsina ya shiga majalisar gudanar da harkokin kamfanin NDPHC mai alhakin harkokin lantarki.

Asali: Legit.ng

People are also reading