Home Back

Kano da Jihohin da Ke Siyan Gas da Tsada, Katsina da Sauki Yayin da Farashin Ya Tashi

legit.ng 2024/5/20

FCT, Abuja - Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa a watan Maris an siyar da gas mai girman 5kg kan kudi N6,591 bayan tashin farashin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wannan karin shi ya ke nuna an samu karin kaso 7.1% idan aka kwatanta da watan Faburairu da ake siyarwa N6,154.

Jihohin da ke siyan gas da tsada da masu siya da araha
Kano na daga cikin jihohin da ke siyan gas da tsada yayin da farashin ya tashi. Hoto: Nurphoto. Asali: Getty Images

Karin da aka samu kan farashin gas

Yayin da a cikin shekara farashin gas ya karu da kaso 42.9% idan aka kwatanta da N4,610 a watan Maris na shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin da ke siya da tsada (5kg)

1. Kano: N7,609.00

2. Ogun: N7,363.64

3. Akwa Ibom: N7,162.50

Jihohin da ke siya da sauki (5kg)

1. Adamawa: N5,312.50

2.Taraba: N5,375.00

3. Zamfara: N5,550.00

Har ila yau, NBS ta ce 'yan Najeriya na biyan N15,929 kan gas mai girman 12kg a watan Maris da ta gabata.

Hakan ya nuna an samu karin kaso 5.7 idan aka kwatanta da watan Faburairu kan N15,060, cewar The Guardian.

Yayin da a cikin shekara farashin ya karu da kaso 55.2% idan aka kwatanta da farkon shekarar bara.

A watan Maris na shekarar 2023 ana siyar da gas mai girman 12kg kan kudi N10, 262 idan aka kwatanta da watan Maris na wannan shekarar da aka siyar kan N15,929, cewar rahoton ThisDay.

Jihohin da ke siya da tsada (12kg)

1. Sokoto: N17,833.33

2. Osun: N17,588.46

3. Anambra: N17,417.65

Jihohin da ke siya da sauki (12.5kg)

1. Katsina: N12,400.00

2. Kebbi: N13,137.50

3. Bauchi: N14,484.25

Wannan karin farashin gas na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke kokawa kan tsadar man fetur da kayan masarufi.

Tashin farashin gas zai yi matukar tasiri ga rayuwar mafi yawan 'yan kasar ganin yadda suka dogara da shi domin yin abinci da sauran abubuwa na yau da kullum.

Dangote ya rage farashin litar dizal

A wani labarin, mun kawo muku cewa matatar man Aliko Dangote ta rage farashin litar dizal ga 'yan Najeriya domin samun sauki.

Matatar ta rage farashin ne daga 1,200 zuwa N1,000 yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin halin matsin rayuwa.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa Aliko Dangote kan wannan mataki inda ya ce hakan zai kawo raguwar farashin kayayyaki.

Asali: Legit.ng

People are also reading