Home Back

Kwararren Hada Bama-bamai Da Wani Mutum Daya Sun Yi Saranda A Borno

leadership.ng 2024/5/19
Sojoji

Wani kwararre kan hada bama-bamai (IED) tare da wani dan ta’adda guda daya, sun mika wuya ga dakarun sashe na 3 na rundunar hadin gwiwa ta MNJTF da ke Monguno ta Jihar Borno.

Wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na rundunar soji ta MNJTF Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, ta ce ‘yan ta’addar sun bayyana sunan Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Garba) dan shekaru 19 kwararre a kan sanin bama-bamai da kuma Bana Modu mai shekaru 13 ya mika wuya a ranar 21 ga Afrilu, 2024.

Abdullahi ya ce, Mohammed da Modu sun bayyana a lokacin binciken farko, cewa an umarce su da su dasa bama-bamai a kan tituna a Doron Baga da Dam Fish da ke Baga, cikin kananan hukumomin Kukawa na Jihar Borno.

Ya ce, “Maimakon su ci gaba da gudanar da aikinsu, sai suka yanke shawarar yin watsi da aikin da suke yi, suka tsere da ‘yan ta’addar tare da mika wuya ga MNJTF.

“Hukumar ta MNJTF ta yi wani yunkuri a kwanan nan inda ta yi wani na OPERATION NASHRUL SALAM, wani aiki na dabarun hadin kai da sassan da suka dace, wanda ke nuna tasirin ayyukan tunani da kwarewa wajen yaki da ta’addanci,” in ji Abdullahi.
Sojojin sun kwato bama-bamai guda biyu, wayoyin hannu guda biyu, da kuma kudi Naira 53,000.00 daga hannun ‘yan ta’addar biyu.

Abdullahi ya ce mika wuyan nasu ya kara jaddada kudirin kungiyar MNJTF na karfafa gwiwar sauran ‘yan ta’addan da ke boye a tsibirin tabkin Chadi su fito su mika wuya da kuma ajiye makamansu, a wani yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

People are also reading