Home Back

Cibiyar Noma Za Ta Samar Da Ingantaccen Irin Farin Wake

leadership.ng 2024/6/28
Cibiyar Noma Za Ta Samar Da Ingantaccen Irin Farin Wake 

Cibiyar kula da harkokin noma ta kasa da kasa (IITA), ta shirya taron bita na kwana biyu; domin sama wa kanannan manoman kasar nan ingantacen Iri na Farin Wake.

Wani kwararre a fannin samar da Irin noma a cibiyar ta IITA, Farfesa Lucky Omoigui ya bayyana cewa, an shirya taron ne don kokarin hada masu ruwa da tsaki a wannan fanni na samar da Irin, domin samun damar tattaunawa kan aikin noma na shekarar 2024 a fadin kasar nan.

Farfesan ya kara da cewa, matsalar da ake samu wajen noma wannan Farin Wake na afkuwa ne sakamakon rashin samun ingantaccen Irin noma.

Ya ci gaba da cewa, a duk shekara a Nijeriya; ana noma Farin Wake kimanin tan miliyan 2.3, duk kuwa da cewa kasar na bukatar wannan Farin Wake sama da tan miliyan 3.

A cewar Lucky, wannan matsala ta rashin samar da isasshen ingantaccen Irin Farin Waken ne ta sa ake shigo da shi daga makwabta kasashen wannan kasa, domin cike gibin da ake da shi.

Ya bayanna cewa, “Ko shakka babu, samar da wannan ingantaccen Irin Farin Wake, zai ba da damar kara yawan nomansa a fadin kasar nan, wanda kuma hakan zai kara samar da dimbin kudaden shiga ga masu nomansa tare da rage yadda ake kashe kudaden”.

Haka zalika, shugaban sashen cibiyar da ke gudanar da aikin cibiyar a Jihar Kano, Dakta Alpha Yaya Kamara a nasa jawabin a wajen taron cewa ya yi, akwai bukatar samar wa da manoma, musamman kananan da ke karkara; ingantaccen Irin Farin Wake.

Shi ma a nasa jawabin a wajen taron, shugaban kungiyar masu hada-hadar Irin noma ta kasa, Yusuf Ado Kibiya (SEEDAN) ya bayyana cewa; kungiyar ta yi hadaka da sauran cibiyoyi domin samar da ingantaccen Irin Farin Wake a fadin wannan kasa.

Ya kara da cewa, a shirye kungiyar take; don yin hadaka da sauran masu ruwa da tsaki, domin samar da ingantaccen Irin wannan Iri na Farin Wake.

People are also reading