Neja: ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masu Ibada a Lokacin Sallar Tahajjud
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Minna, jihar Neja - A daren ranar Juma'a ne wasu mahara suka tare hanyar Kuta da ke Minna babban birnin jihar Neja, inda suka far wa mutanen da ke zuwa sallar Tahajjud.
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na dare a lokacin da Musulamai ke fitowa yin sallar Tahajjud.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daya daga cikin mazauna garin, Aliyu Isah, ya ce ‘yan bindiga dauke da mugayen makamai sun yi garkuwa da mazauna garin Minna tsawon kwanaki biyar da suka gabata.
Ya ce yankunan da suka fi kai wa farmaki sun hada da Kpakungu, Soje, Anguwan Daji, Limawa, Ogbomosho da dai sauransu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Vanguard, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ‘yan sanda na kan gaba a lamarin.
“Rundunar ‘yan sanda na sintiri a kodayaushe suka samu rahoton bullar 'yan bindigar, kuma ana kama su a duk inda abin ya faru."
- Wasiu Abiodun
A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun shiga har cikin masallaci sun sace masallata a jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa nasallatan na sallar Tahajjud ne a lokacin da 'yan bindigar suka farmake su, inda har wasu suka jikkata.
Tun bayan shigowar watan Ramadan, an samu rahotanni da dama na kai hare-hare kan masu ibada a jihohin Arewa, musamman a kwanaki goma na karshe da ake fita sallar Tahajjud.
Asali: Legit.ng