Home Back

Barcelona Ta Sallami Kocinta Xavi Hernández, Ta Bayyana Wanda Zai Maye Gurbinsa

legit.ng 2024/6/26
  • Xavi Hernández zai bar aikinsa na kocin Barcelona bayan wasan karshe na kakar wasa ta bana a ranar Lahadi, in ji kungiyar
  • Xavi, wanda ya buga wa Barça wasanni sama da 700 a matsayin dan wasa, ya karbi ragamar horar da kungiyar a shekarar 2021
  • An ce tsohon kocin Bayern Munich da Jamus, Hansi Flick zai maye gurbin Xavi Hernández, amma za a fitar da sanarwa kan hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernández bayan shafe shekaru uku yana aiki, inda tsohon kocin Bayern Munich da Jamus, Hansi Flick zai maye gurbinsa.

Barcelona ta yi bankwana da Xavi Hernández
Barcelona ta kori Xavi Hernández, za ta maye gurbinsa da Hansi Flick. Hoto: @FCBarcelona Asali: Twitter

Kocin dan kasar Spain mai shekaru 44, zai jagoranci wasan karshe da Barcelona za ta buga da Sevilla a ranar Lahadi kafin ya bar kungiyar.

Barcelona ta sallami kocin ta Xavi

Shafin SkySport ya ruwaito cewa Barcelona ta kori Xavi wata guda bayan da ta lallashe shi ya ci gaba da zama kocinta a lokaycin da ya fara shirin barin kungiyar a karshen wannan kakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton BBC, Barcelona ta cimma yarjejeniya ta baki da Flick domin ya zama koci bayan tafiyar Xavi.

Kungiyar ta Spain ta ce tana shirin bayar da sanarwa game da wanda zai maye gurbin Xavi nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Sanarwar da kungiyar ta Catalan ta fitar ta ce:

"FC Barcelona na son godewa Xavi saboda aikin da ya yi a matsayin koci, da kuma yadda ya taka rawar gani a matsayinsa na dan wasa da kuma kyaftin din kungiyar."

Nasarorin Xavi a matsayin kocin Barcelona

Xavi Hernández ne zai jagoranci wasan da Barcelona za ta yi da Sevilla a ranar Lahadi a wasansa na karshe a matsayin koci, in ji rahoton ESPN.

Xavi zai bar Barcelona yayin da kungiyar ta ke a matsayi na biyu a kan tebur, ya kuma kai kungiyar zuwa wasan kusa dana karshe na gasar zakarun Turai amma ta sha kashi a hannun Paris Saint-Germain.

Gabaɗaya dai, Xavi Hernández ya lashe kofin La Liga a 2023 sannan kuma ya ɗaga Super Cup na Sipaniya bayan 'yan watanni.

Tony Kroos zai yi ritaya daga buga kwallo

A wani labarin, mun ruwaito cewa

Asali: Legit.ng

People are also reading