Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2024

bbc.com 2024/7/6

Rahoto kai-tsaye

Al'ummar Musulmi a faɗin duniya na bukukuwan Babbar Sallah

,

Al'ummar Musulmi a faɗin duniya na gudanar da shagulgulan Babbar Sallah.

A jiya ne da Mahajjata suka gabatar da tsayuwar Arfa a Saudiyya, inda yau kuma suke gabatar da Dawafi a ɗakin Ka'aba.

A Najeriya a wasu sassan ƙasar an wayi gari da ruwan sama, inda a wasu wuraren aka yi Sallar Idin a masallatan Juma'a.

Alal misali a jihar Kano da ke arewacin ƙasar gwamnan jijar Abba Kabir Yusus ya halarci sallar ne a masallacin Shehu Tijjani na kusa da masallacin Idi na kofar Mata.

Yayin tattaunawara da BBC, Gwamna Abba Kabir ya yi kira ga al'ummar jihar su ci gaba da gudanar abubuwan da suka kamata na kaunar juna da inganta harkokin addini.

People are also reading