Gwamna Ya Dauki Tsattsauran Mataki Kan Masallatai da Coci a Plateau, Ya Kakaba Wata Doka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta dauki mataki kan masallatai da coci da ke tare hanyoyi yayin ibada.
Gwamna Caleb Mutfwang shi ya tabbatar da haka inda ya ce ya haramta kange hanyoyi da ake yawan samu a jihar lokacin ibada.
Daily Trust ta ruwaito cewa Caleb ya kuma bukaci duka wuraren ibada su mika takardun amincewa da hukumar kula da birane (JMDB) ta ba su yayin gina wuraren ibadun.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin babban manajan hukumar, Hart Bankat.
An rubuta takardun ga kungiyar Kiristoci ta CAN da Jama'atul Nasril Islam (JNI) da ke jagorantar addinan biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin bayani na tafe...
Asali: Legit.ng