Home Back

Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi

leadership.ng 2024/6/26
Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi

Karbuwar hajojin kasar Sin masu nasaba da sabbin makamashi a kasuwannin duniya, ba shi da wata nasaba da tallafin gwamnati ga fannin, maimakon haka, karin shigar hajojin kasuwannin kasa da kasa, na da alaka ne da tsawon lokaci da kamfanonin kasar ta Sin suka shafe suna aiki tukuru.

Da yake bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yadong, ya ce kamfanonin kasar Sin sun shafe sama da shekaru 20 suna zuba jari a fannonin bincike da samar da ci gaba, a sassan sabbin makamashi. Kaza lika, ta hanyar fafata takara a kasuwa, sun kai ga samun fifiko na musamman.

He Yadong, ya ce “Sashen kasuwannin sabbin makamashi na kasar Sin cike yake da takara, wadda ta haifar da kaiwa ga nasara ga mafi karko, da ma ci gaban da ake samu na bullar kamfanoni masu ingancin fasahohi da hajoji”.

Game da manufofin baiwa masana’antun tallafi kuwa, kakakin ya ce, kasashen yamma ne asalin wadannan manufofi, kafin daga bisani sauran kasashen duniya su ara su yafa.

Ya ce, manufofin baiwa kamfanonin Sin tallafi, sun dace da ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, suna kuma bin ka’idojin daidaito, gudanar da komai a bude, da kaucewa nuna bambanci. A daya bangaren kuma, dukkanin kamfanonin dake hada-hada a cikin kasar Sin na cin gajiya ta bai daya a wannan fanni. (Saminu Alhassan)

People are also reading