Home Back

An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi A Adamawa

leadership.ng 2024/8/25
An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi A Adamawa

Babbar Alkalin Alkalan Jihar Adamawa, Mai Shari’a Hafsat Abdulrahman, ta rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomin jihar 21, a ranar Litinin 15 ga watan Yuli, 2024.

Hakan ya biyo bayan zaben da hukumar zabe ta jihar (ADSIEC) ta gudanar a ranar Asabar 13 ga watan Yuli, inda jam’iyyar PDP ta lashe dukkan kujerun shugabannin 21 da na kansiloli 225 yayin da jam’iyyar NNPP, ta samu kujerar kansila daya a karamar hukumar Demsa.

Da yake jawabi a taron gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya kalubalanci shugabannin da su guji hanci da cin rashawa tare da rungumar kowa da kowa a gwamnatinsu.

Gwamnan ya kuma gargadi sabbin shugabannin da kansiloli da su guji rashin zuwa aiki akan lokaci, domin gwamnati mai ci ba za ta lamunci irin wannan dabi’a ta yadda shugaba zai yi watsi da aikinsa ba tare da wani dalili ba.

Gwamna Umaru Fintiri ya jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ADSIEC bisa gudanar da zaben da aka amince da shi a matsayin wanda ya fi kowanne inganci a tarihin jihar Adamawa.

Haka kuma gwamnan ya taya shuwagabannin jam’iyyar PDP da shugabannin murnar nasarar da suka samu a lokacin zaben, ya bukaci jama’a da su ci gaba da kasancewa masu biyayya da goyon baya ga gwamnatinsa domin ci gaban al’ummar jihar.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Barista A T Shehu a jawabinsa, ya tunatar da shugabannin da aka rantsar cewa an zabe su ne bisa mutuncin gwamna Umaru Fintiri, inda ya bukace su da su yi koyi da shi tare da samar da shugabanci na gari.

A jawabin godiya a madadin takwarorinsa, Suleiman Ahmed, sabon shugaban karamar hukumar Toungo, ya ce wa’adin da suke dashi na shekara biyu, ba zai wadatar ba muddin ba tare da kyakkyawan shugabancin gwamna Fintiri ya shimfida ba.

Ya kuma jaddada aniyarsu na gudanar da ayyukansu da kuma aiki bisa tsarin ci gaban wannan gwamnati mai ci domin amfanin al’ummar Adamawa.

People are also reading