Kungiyar Tarayyar Turai Ta Kakabawa Iran Sabon Takunkumi Kan Harin da Ta Kai Isra’ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta amince da sanyawa kasar Iran takunkumi biyo bayan harin ramuwar gayya da ta kai Isra'ila.
Shugabannin sun amince da sabon takunkumin ne a wani taro da suka gabatar a birnin Brussels domin daukan mataki akan harin da Iran ta kaiwa Isra'ila ranar Asabar.
Sabon takunkumin zai shafi kere-keren da Iran ke yi ne na jirage marasa matuka da makamai masu linzami wanda da su ta kai hari zuwa Isra'ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa sabon takunkumin ya zo ne bayan takunkumin hana Iran sayar da jirage marasa matuka wa tarayyar Rasha tun bayan fara yakinta da Ukraniya.
Tin bayan da Iran ta kai harin ramakon dai Isra'ila ta rinka kira ga kawayenta domin daukan mataki akan Iran, cewar jaridar Al-Jazeera.
A wurin taron, shugaban kungiyar tarayyar Turai, Charles Michael, ya tabbatar da cewa dole ne su mayar da Iran saniyar ware saboda abinda ta aikata, cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Tun bayan harin ramakon da Iran ta kai ranar Asabar, har yanzu Isra'ila ba ta dauki matakin soji domin mayar da martanin ba.
A wani rahoto kuma, kun ji cewa kasar Saudiyya ta musanta tallafawa Isra'ila wurin kakkabo jiragen yakin da Iran ta harba mata ranar Asabar data wuce.
Kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar ne biyo bayan jita-jita da ake yadawa a kan tana cikin kasashen da suka tallafawa Isra'ila a lokacin harin.
Asali: Legit.ng