Home Back

Taron NATO ya shiga kwanaki na uku

dw.com 2024/8/24

A ci gaba da taron shugabannin kasashen kungiyar taron NATO/OTAN da ke gudana a kasar Amirka, ana sa ran a wannan Alhamis Shuigaba Volodymyr Zelensky na Ukraine da kasarsa take fuskantar kutse daga Rasha zai gana da shugabannin kungiyar tsaron. Kungiyar tsaron tana kuma duba irin sabon kalubalen da ake fuskanta daga China a yankin nahiyar Asiya.

Taron na kwanaki uku yana gudana a kasar Amirka daidai lokacin da kungiyar tsaron ta NATO ke cika shekaru 75 da kafuwa, inda yanzu take da mambobi 32, kuma take zama kawancen tsaro mafi girma da tasiri a duniya.

Sai dai taron na zuwa lokacin da siyasar kasar ta Amirka ta rincabe yayin da ake shirin zaben shugaban kasa nan gaba cikin wannan shekara, saboda cece-kuce kan ko Shugaba Joe Biden na Amirka yana da kuzarin da zai iya ci gaba da tafiyar da kasar, a daya bangaren kuma zai fafata ne da tsohon Shugaba Donald Trump wanda ya yi kaurin suna wajen kalamai masu tayar da kura. Duk da wannan yanayi Sakatren harkokin wajen kasar ta Amirka Antony Blinken ya kawar da shakku kan kudirin kasashen na NATO na taimakon Ukraine, yayin da yanzu haka wasu kasashen kungiyar suka taimaka da wasu jiragen saman yaki na zamani, domin fuskantar kutsen daga Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

People are also reading