Home Back

Nijar ta dakatar da tunkuda man fetur dinta zuwa Benin

dw.com 2024/7/2
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da tunkuda danyen man fetur dinta cikin bututun da ke zuwa Jamhuriyar Benin, sakamakon takun saka da rikicin diflomasiyya da ke kara zafi tsakanin makwabtan kasashen biyu.

Ministan man fetur din kasar Mahamane Moustapha Barke ne ya sanar da hakan, lokacin da ya ziyarci cibiyar tunkudo danyen man, don cika umarnin shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdourahmane Tiani na rufe ta.

A makon da ya gabata ne dai hukumomin Jamhuriyar Benin suka kama jami'an kamfanin man fetur din Nijar guda biyar, inda suka zargi biyu daga cikinsu da cewa 'yan leken asirin gwamnatin sojin Nijar din ne, amma suka yi badda bami a matsayin ma'aikatan kamfanin man fetur din WAPCO na Chaina.

People are also reading