Home Back

Yadda hare-haren ƴan bindiga ke zafafa a birnin Gwari

bbc.com 5 days ago
.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Yayin da masana ke gargadin samun ƙarancin abinci a bana a Najeriya, manoman da ke zaune a yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna, na bayyana damuwa game da yadda ake samun ƙaruwar yawan hare-haren da 'yan bindiga musamman a kan manoma.

Wasu daga cikin manoman da ke yankin sun ce wannan al'amari ya sa da yawansu sun daina zuwa gona sun koma zaman gida, al'amarin da ake ganin zai iya ƙara munana matsalar ƙarancin abinci da yanzu haka ake fama da ita a ilahirin ƙasar.

Wannnan na faruwa ne a dai dai lokacin da damuna ke kankama a arewacin Najeriya, lokacin da ya kamata manoman su dukufa wajen shuka, sai dai wani daga cikin monoman yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa 'A cikin sati biyun da suka gabata a kullum sai sun dauki mutane, kama daga kauyukan Randagi, da Kakangi, da Dagara, da Rema, da Bugai, a kullum haka muke fama, abin ya wuce dukkan yadda ake tunani" in ji manomin

Shi ma wani manomi ya ce a baya a baya jama'ar garuruwan na yankin Birnin Gwari sun sha yin sulhu tare da kulla yarjejeniya da 'yan bindigar don su bar su su yi noma, amma sai daga baya su saba alkawari''

“Dukkan wani kauye da yan bindigar na ke ki hari babu inda ba a yi sulhu da su ba, amma hakan bai hana su ci gaba da tatsar kudi daga hannunmu ba, ba sa mutunta sulhun da muka yi da su''

Haka kuma ya ce “bamu san yadda damunar za ta kasance ba, tunda ga yadda muke fama da tsadar kayan noman, don da ƙyar manoma su fita gona, don kuwa iya kashi talatin da biyar (35) cikin ɗari na monoma yankin ne kaɗai ake sa ran zasu iya yin noma''

Muna daukar matakai kan Lamarin

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana sane da wannan hali da jama'ar na yankin Birnin Gwari ke ciki, kuma ba ta yi kwance da sirdi ba.

Samuel Aruwan, shi ne kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ya ce "gwamanti da jami''an staro muna nan muna bakin kokarin mu muna fafatawa da ƴan bindigar", inji shi.

Yankin na Birnin Gwari dai ya zama tamkar wani babban ɗan yatsa ne a harkar noma, wanda galibi aka yi ittifaki cewa yana sahun gaba wajen samar da kayan amfanin gona na ci da na sayarwa masu dimbin yawa, ba wai ga ga jama'ar gida Najeriya kadai ba, har ma da kasashen ketare, al'amarin da matsalar tsaro ke ta zai-zayewa shekara da shekaru.

’Yan bindigar dai sun jima suna kai hare - hare wadannan yankuna, to amma a yanzu lamarin ya munana saboda ga alama suna neman mamaye yankunan ne da nufin sanya ka’idojin gudanar da rayuwa.

Duk da ikirarin da jami’an tsaro ke yi na shawo kan matsalar ‘yan fashin daji, har yanzu ba su daina kai hare - hare yankunan jihar ba.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ta'ajibi kan matakin da fitaccen ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen addabar jama'a a arewacin Najeriya Dogo Giɗe, fara ba wa manoma kariya don su koma gonakinsu a jihar Zamfara.

Manoma a ƙananan hukumomin Tsafe, da Maru da ke Zamfara, da ma wani ɓangare na yankin ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina, sun shaida wa BBC cewa sun zauna da Dogo Giɗen, kuma ya musu alkawarin kare su daga sauran gungun ƙungiyoyin ƴan bindigar da a baya suka hana su noma a gonakinsu.

People are also reading