Home Back

Shugaba Biden ya ce Ukraine za ta yi galaba a kan Rasha

bbc.com 2024/8/24
Joe Biden

Asalin hoton, Reuters

Shugaban Amurka Joe Biden ya kaddamar da taron kolin kungiyar tsaro ta NATO na 75, tare da alkawarin sama wa Ukraine karin makamai don kare kanta daga Rasha.

A jawabin bude taron kolin, dan takaitacce, amma mai karfi, Mista Biden, ya ce a yanzu NATO ta yi karfi fiye da a baya, yayin da take fuskantar yaki tsakanin Rasha da Ukraine;

Shugaban na Amurka ya kaddamar da taron kolin na shugabannin NATO a Washington, cikin wani jawabi mai karfi inda yake, gwarzanta kansa kan fadadar kungiyar tsaron da kuma samar da karin kudade da kayan aiki da kawancen ke yi.

A jawabin ya nemi kara tabbatar wa da abokan tafiya na waje da na cikin gida cewa zai iya yakar babban kalubalen zabe da ke gabansa da Donald Trump.

Mista Biden, ya ce a yanzu NATO ta yi karfi fiye da a baya, yayin da take fuskantar yaki tsakanin Rasha da Ukraine; yana sanar da bayar da karin tallafin soji ga Ukraine.

Shugaban na Amurka tare da takwarorinsa na Jamus da Italiya da Netherlands da Romania sun bayyana cewa za su bai wa Ukraine makaman kariya ta sama domin kara karfafa mata garkuwa da ta yi rauni.

Mista Biden ya ce yakin zai kare inda Ukraine za ta ci gaba da kasancewa kasa mai ‘yanci.

Sai dai kuma dukkanin alkawuran na Shugaba Biden kusan bai kwantar wa da Shugaba Zelensky na Ukraine hankali ba yadda yake so.

Mista Zelensky da ke jawabi a wani wajen daban ya mayar da hankalinsa ne kan neman Amurka ta kyale kasarsa ta yi amfani da makaman da take ba ta taimako ta kai wa Rasha hari kai tsaye cikin kasar.

Abin da Shugaba Biden ya dade da ki saboda daukar hakan a matsayin wata tsokana ga Moscow.

People are also reading