Home Back

Gaskiya Ta Fito, Tsarin Sabon Naira da Tsohon Gwamnan CBN Ya Yi Ba Irinsu Buhari Ke So Ba

legit.ng 2024/7/3
  • Tsohon gwamnan CBN ya kara shiga matsala sabuwa yayin da bayanai ke ƙara fitowa kan tsarin sauya fasalin Naira
  • Tsohon daraktan harkokin kuɗi a CBN, Ahmed Umar, ya shaidawa kotun Abuja cewa Emefiele ya buga kalar sababbin kuɗin da ya ga dama ba wanda Buhari ya amince ba
  • Wannan na zuwa ne bayan EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a gaban kotu kan tuhume-tuhume huɗu a watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Tsohon daraktan harkokin kuɗi a babban bankin Najeriya (CBN), Ahmed Umar, ya ci gaba da bayanin yadda aka yi canjin takardun Naira a mulkin Buhari.

Ahmed ya bayyana cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya buga kalar takardun Nairan da ya ƙirƙiro amma ba su shugaban ƙasa ya bayar da umarni ba.

Emefiele da Buhari.
Tsohon daraktan CBN ya bayar da shaida a gaban kotu kan canjin kuɗin Emefiele Hoto: @GodwinIEmefiele Asali: Twitter

Idan baku manta ba a ranar 15 ga watan Mayu, 2024, hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Emefiele kan tuhume-tuhume huɗu a babban kotun tarayya a Abuja.

Kamar yadda The Nation ta kawo, ana zargin Emefiele da shure tanadin doka wajen aiwatar da tsarin canja takardun N200, N500 da N1000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan ana tuhumarsa da yin gaban kana wajen canjin kuɗin ba tare da sahalewar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da majalisar gudanarwa ta CBN ba.

Sai dai Mista Emefiele ya musanta aikat ko ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa, inda kotu ta bayar da belinsa kan N300m.

Da yake ɓayar da shaida a kotu, Ahmed Umar ya ce zanen da ke jikin kalar kuɗinnda Buhari ya amince ya sha bamban da kalar da Emefiele ya sa aka buga.

"Tsaron sabon kuɗin da Buhari ya amince da shi yana da lambar QR Kod amma kuɗin da ke yawo a yanzu wanda Emefiele ya kirkiro ba su da shi.

"Haka nan an amince a sa hoto a ɓangaren dam amma CBN ya buga a hagu kuma tsarin lambobin jikin takardun kuɗin ya sha bambam da yadda shugaban ƙasa ya bayar da umarni."

A wani rahoton kuma

Asali: Legit.ng

People are also reading