An Kwace Kwangilar Hanyar da ta Haɗa Arewa da Kudu Hannun Dantata da Wasu Kamfanoni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ministan ayyuka na kasa,Nweze David Umahi ya sanar da dakatar da kwangilar hanyar data haɗa jihohin Kogi da Edo.
Gwamnatin tarayya ta ba kamfanoni uku kwangilar aikin biyunta titin tun shekarar 2012 amma sun gagara karasa aikin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hadimin ministan ayyuka, Barista Orji Uchenna ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan da ma'aikatar ayyuka ta kasa ta fitar ya nuna cewa kamfanin ayyuka na Dantata and Sawoe Construction na cikin wadanda aka ba kwangilar.
Cikin kamfanonin da aka ba kwangilar har ila yau akwai kamfanin ayyuka na Mothercat Ltd da RCC Ltd, rahoton jaridar Punch.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kwace kwangilar ne sakamakon tafiyar hawainiya da aikin ke yi tun da aka fara shi a shekarar 2012.
Ta kuma kara da cewa rashin tafiyar aikin yadda ya kamata na cigaba da kawo rashin jin dadi ga mutane da suke tafiya a kan hanyar.
Ministan ya ba injiniyoyin ma'aikatar umurnin gaggauta karbar dukkan bayanan aikin daga kamfanonin domin samun yadda za a cigaba.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin ba za ta yi wasa ba wajen dakatar da duk wanda aka ga yana tafiyar hawainiya da kwangila da aka ba shi.
A wani rahoton, kun ji cewa David Umahi bai ji dadin aikin da ya gani a titin Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia ba.
Rahotanni sun nuna cewa Ministan ayyukan na Najeriya ya soki kamfanin Fig Fyne Construction Company da aka ba kwangilar.
Asali: Legit.ng