Home Back

NDLEA Ta Kama Basarake da Ɗan NYSC Kan Zargin Safarar Kwaya

legit.ng 2024/10/6
  • Hukuma mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cakfe wadanda ake zargi da laifuffuka da dama a sassan Najeriya
  • Cikin mutanen da hukumar da cafke akwai basarake da mai hidimar kasa ta NYSC da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya
  • NDLE ta kai samame kan masu laifi ne a garuwawa da dama wanda suka haɗa da jihohin Kano, Legas, Benue Yola, Enugu da Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukuma mai yaki da safarar kwaya ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar cafke miyagu a garuruwa da dama.

Cikin waɗanda hukumar ta cafke akwai wani basarake a Osun da mai hidimar kasa ta NYSC a jihar Kano.

NDLEA
NDLEA ta kama miyagu a jihohi. Hoto: NDLEA Asali: Facebook

Legit ta tatttaro labarin ne cikin wani sako da hukumar NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook a jiya Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Safarar kwaya: NDLEA ta kama basarake

Hukumar NDLEA ta sanar da cafke Ba'ale Ige Babatunde da tabar wiwi da ta kai nauyin kilo biyar.

Basaraken, Ba'ale Ige Babatunde mai shekaru 50 yana sarauta ne a Akaranbata da ke yankin Ile-Ife a jihar Osun.

Safarar kwaya: NDLEA ta kama ɗan NYSC

A wani samamen da hukumar NDLEA ta kai a jihar Kano ta cafke dan bautar ƙasa, Yusuf Abdulrahman.

NDLEA ta kama Yusuf Abdulrahman ne a gidan masu hidimar kasa da ke karamar hukumar Sumaila a jihar Kano bisa zargin safarar kwaya.

NDLEA ta kama miyagu a jihohi

Haka zalika hukumar NDLEA ta yi nasarar cafke wasu masu safarar kwaya a jihar Legas wanda Agbakoba John Mmadu da Agbakoba Ijeoma Chinyere ke jagoranta.

Har ila yau, hukumar ta cafke mutane da dama a Abuja, Benue, Adamawa, Enugu da sauransu, rahoton Aminiya.

NDLEA ta kawo shawarar gwajin kwayoyi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayar da shawara kan yadda za a rage rabuwar aure a jihar Kano.

Shugaban hukumar a Kano, Abubakar Idris Ahmad ya bayar da shawarar a rika tilasta gwajin kwaya gabanin aure domin kakkabe al'adar.

Asali: Legit.ng

People are also reading