NDLEA Ta Kama Basarake da Ɗan NYSC Kan Zargin Safarar Kwaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Hukuma mai yaki da safarar kwaya ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar cafke miyagu a garuruwa da dama.
Cikin waɗanda hukumar ta cafke akwai wani basarake a Osun da mai hidimar kasa ta NYSC a jihar Kano.
Legit ta tatttaro labarin ne cikin wani sako da hukumar NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook a jiya Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar NDLEA ta sanar da cafke Ba'ale Ige Babatunde da tabar wiwi da ta kai nauyin kilo biyar.
Basaraken, Ba'ale Ige Babatunde mai shekaru 50 yana sarauta ne a Akaranbata da ke yankin Ile-Ife a jihar Osun.
A wani samamen da hukumar NDLEA ta kai a jihar Kano ta cafke dan bautar ƙasa, Yusuf Abdulrahman.
NDLEA ta kama Yusuf Abdulrahman ne a gidan masu hidimar kasa da ke karamar hukumar Sumaila a jihar Kano bisa zargin safarar kwaya.
Haka zalika hukumar NDLEA ta yi nasarar cafke wasu masu safarar kwaya a jihar Legas wanda Agbakoba John Mmadu da Agbakoba Ijeoma Chinyere ke jagoranta.
Har ila yau, hukumar ta cafke mutane da dama a Abuja, Benue, Adamawa, Enugu da sauransu, rahoton Aminiya.
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayar da shawara kan yadda za a rage rabuwar aure a jihar Kano.
Shugaban hukumar a Kano, Abubakar Idris Ahmad ya bayar da shawarar a rika tilasta gwajin kwaya gabanin aure domin kakkabe al'adar.
Asali: Legit.ng