Home Back

'Yan Bindiga Sun Sace Manajan Kamfani da 'Yan Kasar Waje a Wani Hari

legit.ng 2024/7/3
  • Wasu miyagun ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da manajan daraktan kamfanin Fouani a jihar Legas
  • Masu garkuwa da mutanen sun kuma yi awon gaba da wasu ƴan ƙasar Lebanon mutum uku waɗanda suke tare da manajan a cikin kwale-kwale
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da manajan darakta na kamfanin Fouani mai wakiltar LG da Hisense a Legas.

Ƴan bindigan sun sace manajan ne tare da wasu ƴan kasar Lebanon guda uku a yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale a Legas.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Legas
'Yan bindiga sun sace 'yan kasar waje a Legas Hoto: @PoliceNG Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun sace mutane a Legas

Ko da yake ba a tantance sunayen wadanda aka sace ba, an ce an yi garkuwa da su ne a kusa da gadar Falomo a lokacin da suke tafiya daga Apapa zuwa Victoria Island, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya mai tushe da ke da masaniya kan lamarin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa jaridar The Punch cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa.

"Jiya (Juma'a) da yamma, an yi garkuwa da manajan darakta na kamfanin Fouani (LG da Hisense) da ƴan ƙasar Lebanon uku a kusa da gadar Falomo yayin da suke tafiya daga Apapa zuwa Victoria Island a cikin kwale-kwale."
"Masu garkuwa da mutanen sun nemi a ba su dala miliyan 1.5 a matsayin kuɗin fansa."

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

"Eh, gaskiya ne. Mun samu rahoton kuma muna bincike a kai. Ku yi haƙuri ba zan iya faɗin abin da ya wuce haka ba."
"A yanzu ba zan iya bayyana suna, yaushe, wuri da yadda lamarin ya faru ba amma muna kan bincike."

- Benjamin Hundeyin

Ƴan bindiga sun sace fasinjoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da dama bayan sun buɗe wuta kan wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 a kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar ne a mahaɗar Bishini, kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

People are also reading