'Yan Bindiga Sun Sace Manajan Kamfani da 'Yan Kasar Waje a Wani Hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da manajan darakta na kamfanin Fouani mai wakiltar LG da Hisense a Legas.
Ƴan bindigan sun sace manajan ne tare da wasu ƴan kasar Lebanon guda uku a yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale a Legas.
Ko da yake ba a tantance sunayen wadanda aka sace ba, an ce an yi garkuwa da su ne a kusa da gadar Falomo a lokacin da suke tafiya daga Apapa zuwa Victoria Island, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya mai tushe da ke da masaniya kan lamarin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa jaridar The Punch cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa.
"Jiya (Juma'a) da yamma, an yi garkuwa da manajan darakta na kamfanin Fouani (LG da Hisense) da ƴan ƙasar Lebanon uku a kusa da gadar Falomo yayin da suke tafiya daga Apapa zuwa Victoria Island a cikin kwale-kwale."
"Masu garkuwa da mutanen sun nemi a ba su dala miliyan 1.5 a matsayin kuɗin fansa."
- Wata majiya
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
"Eh, gaskiya ne. Mun samu rahoton kuma muna bincike a kai. Ku yi haƙuri ba zan iya faɗin abin da ya wuce haka ba."
"A yanzu ba zan iya bayyana suna, yaushe, wuri da yadda lamarin ya faru ba amma muna kan bincike."
- Benjamin Hundeyin
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da dama bayan sun buɗe wuta kan wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 a kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar ne a mahaɗar Bishini, kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng