Home Back

Dalilin Da Ya Sa Za a Yi Wa Tsohuwar Ministar Jin Ƙai Titsiye Kan Biliyan ₦729b

leadership.ng 2024/10/6
Dalilin Da Ya Sa Za a Yi Wa Tsohuwar Ministar Jin Ƙai Titsiye Kan Biliyan ₦729b

Babbar Kotun Tarayya a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Deinde Dipeolu, ta umurci tsohuwar Ministar Harkokin jin ƙai Hajiya Sadia Umar-Farouk, da ta bayyana cikakkun bayanai na yadda aka rarraba N729 biliyan ga ‘yan Najeriya miliyan 24.3 cikin watanni shida. Wannan hukuncin ya zo ne sakamakon ƙarar ƴancin samun bayanai da ƙungiyar SERAP ta shigar.

A cikin hukuncinsa, Mai Shari’a Dipeolu ya umurci tsohuwar ministar da ta bayar da jerin sunayen waɗanda suka ci gajiyar kuɗaɗen, yawan jihohin da suka samu tallafin, da kuma yadda aka rarraba kuɗaɗen a kowace jiha.

Ya kuma umurci Hajiya Umar-Farouk da ta bayyana sharuɗɗan da aka yi amfani da su wajen zaɓen waɗanda suka ci gajiyar kuɗaɗen da kuma hanyoyin biyan kuɗin. Kotun ta nemi ƙarin bayani kan yadda aka ware ₦5,000 ga kowanne Mutum daga cikin mutanen miliyan 24.3, wanda ke wakiltar kashi biyar cikin ɗari na kasafin kuɗin Najeriya na 2021 wanda ya kai Naira tiriliyan #13.6t.

Mai Shari’a Dipeolu ya yi watsi da hujjojin da lauyan tsohuwar ministar ya gabatar, ya jaddada cewa ƙin bayyana bayanan da ake nema ba shi da uzuri. Ya ƙara da cewa rashin bin dokokin da kotun ta shinfiɗa za a ɗauke shi a matsayin bijirewa.

Yayin da yake mayar da martani kan neman a soke tuhumar ministar, Mai Shari’a Dipeolu ya yi nuni da buƙatar doka ta cewa dole ne hukumomin gwamnati su amsa buƙatun bayanai cikin kwanaki bakwai, kamar yadda dokar ‘Yancin Samun Bayanai ta tanada ta FOI.

Ya kammala da cewa ƙarar da SERAP ta shigar ta bi ƙa’ida cikin lokacin da ya dace, don haka ya yi watsi da ikirarin cewa an shigar da ƙarar bayan ta sauka daga minista.

People are also reading