Home Back

Kotu ta ce Sadiya ta bayar da bayanan yadda ta raba Naira biliyan 729 ga marasa galihu miliyan 24.3, cikin watanni shida

premiumtimesng.com 2024/10/6
BIN DIDDIGI: Shin da gaske ne gwamnati ta kashe naira biliyan 5.9 wajen horas da matasa 177 kan gyaran wayar hannu?

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ta umarci tsohuwar Ministar Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Farouq ta fayyace yadda aka yi ta raba Naira biliyan 729 ga mutum miliyan 24.3 a cikin watanni shida kaɗai.

Haka kuma kotun ta umarci tsohuwar ministar ta zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ta bayar da jadawalin sunayen talakawa da marasa galihun da aka ce sun ci moriyar tallafin. Kuma a je da cikakken bayanin jihohin da suka ci moriyar tallafin da adadin da aka raba a kowace jihar.

Cikin watan Yuni ne dai Mai Shari’a Deinde Dipeolu ta yanke wannan hukunci, biyo bayan wata ƙarar ‘yancin nema, tambaya da bayar da bayanan ayyukan hukumomin gwamnatin tarayya da aka shigar a kotun, ƙara mai lamba FHC/L/CS/853/2021, wadda ƙungiyar SERAP ta shigar, kuma wannan jarida ta samu kwafen takardun shari’ar a ranar Juma’a.

A hukuncin da ya yankez Mai Shari’a Dipeolu ya ce, “Tilas tsohuwar Ministar ta bayar da dukkan bayanan da ake nema ga ko ma wane ne ya nema, ciki har da SERAP.

“Saboda haka na bayar da umarnin tilas daga wannan kotun cewa ina umarta tare da tilasta wa tsohuwar ministar ta bayar da bayanin yadda ta ce ta raba Naira biliyan 729 ga marasa galihu su miliyan 24.3 cikin 2021.”

Mai Shari’a ya ce Sadiya ta bai wa SERAP cikakken bayanin irin tsarin da aka bi wajen zaɓen waɗanda suka ci gajiyar tallafin.”

“Mai Shari’a ya ce Sadiya ta yi bayanin fa’idar raba Naira 5,000 ga ‘yan Najeriya su miliyan 24.3 kowanen su a cikin 2021, adadin da ya kai kashi 5 bisa 100 na Kasafin Najeriya na Naira tiriliyan 13.6.

Da farko lauyan toahuwar Minista Sadiya ya nemi ya kawo togaciya, amma Mai Shari’a ya ce sai fa Sadiya ta bayar da bayanin.

People are also reading