Home Back

RIKICIN SIYASAR RIBAS: Rikicin Gwamna Fubara da Wike zai iya kawo naƙasu ga yankin Neja Delta – Jonathan

premiumtimesng.com 2024/9/28
Yadda Gwamna Fubara ya tada ‘ƙwanƙwamai’ da ‘albatsutsan’ Akpabio, har ya riƙa ‘tambotsai’ wurin rufe gawar attajiri Wigwe

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas da tsohon ubangidan sa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nysom Wike cewa su ajiye saɓanin da ke tsakanin su gefe ɗaya su sasanta tsakanin su.

Gwamna Fubara da Ministan FCT Abuja sun samu babban saɓani, tun cikin Oktoba, 2023 lokacin da wasu ‘yan majalisar dokokin
Jihar Ribas masu goyon bayan Wike, suka yi yunƙurin tsige Gwamna Fubara.

Dangantaka tsananin Fubara da Wike ta ƙara yin dameji sosai, ta yadda sulhun da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi masu, bai yi wani tasiri ba.

Tinubu ya shiga tsakani bayan da aka ayyana cewa dukkan ‘yan Majalisar Dokoki da suka fice daga PDP suka koma APC, to babi su babu muƙaman su.

A majalisar Ribas dai mambobin uku ke kaɗai masu zaman majalisa, yayin da kotu ta haramta wa su 27 shiga cikin majalisa, saboda sun yi canjin sheƙa zuwa APC.

Yayin da Jonathan ke jawabi a lokacin da ya ƙaddamar da fara titin Hanyar Trans-Kalabari, a ranar Litinin.

Jonathan, wanda ya yi shugabancin Najeriya tsakanin 2010 zuwa 2015, kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa mai maƙautaka da Ribas, ya roƙi Gwamna Fubara da Ministan FCT Abuja, Wike su sasanta domin a samu zaman lafiya a Ribas.

Ya ce Jihar Ribas ita ce tamkar zuciya a gangar jikin Yankin Neja Delta, idan ta lalace, to yankin Neja Delta zai lalace.”

“Idan Jihar Ribas ta afka cikin rikici, to zai shafe dukkan yankin baki ɗaya. Kuma ba yankin Neja Delta kaɗai abin zai shafa ba.”

Jonathan ya kuma yi kira ga manya su ci gaba da sa baki har a samu sasanci tsakanin tsohon gwamna Wike da Gwamna Fubara, wanda ya gaje shi.

People are also reading