Home Back

Jirgin Shugaban Kasa Na Ci Gaba Da Lakume Makudan Kudade Wajen Kula Da Shi

leadership.ng 2024/4/27
Jirgin Shugaban Kasa Na Ci Gaba Da Lakume Makudan Kudade Wajen Kula Da Shi

Ana ci gaba da nuna matukar damuwa kan irin makuden kudaden da jirgin shugaban kasan Nijeriya ci gaba da lakume biliyoyin naira.

Wani babban jami’in da ke da cikakken masaniya kan yadda ake kula da jirgin shugaban kasan ya shaida cewa a tsakanin kula na yau da kullum da sayen wasu abubuwan da jirgin ke bukata, tabbas jirgin na lakume makudan kudade fiye da kima.

Ya ce, ba wani sabon abu ba ne kan yadda makudan kudaden ke tafiya da sunan kula da jirgin, wanda a hakan ne ma wani tsohon kwamandan tukin jirgin shugaban kasa ABM AA Yaro, ya bada shawarar a daina amfani da jirgin zai fi wa kasar nan amfani.

Jirgin mai lamba ‘Air Force 001 kirar 737 Boeing Business Jet (BBJ) da aka sayo zamanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a kan kudi dalar Amurka miliyan 43.

Jirgin wanda kayan kula da shi ke kara tsada kamar sauran jiragen zamani da ake kerawa.

Idan za a tuna dai, ‘yan watanni kalilan da karewar wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari aka tura jirgin domin a yi masa gyara ta musamman gabanin rantsar da Shugaban kasa Bola Tinubu.

Sai dai kuma duk da bayan wannan gyaran kwaf da aka yi wa jirgin, har zuwa yanzu jirgin ana ci gaba da turasa domin a yi masa gyaran da aka tsara da kuma wanda ma ba a tsara ba.

Wata majiya mai karfi daga bangaren masu tuka jirgin shugaban kasa ta tabbatar da cewa jirgin ya handame dala miliyan 5 na kudaden gyarasa da kula da shi, kusan rabin sama da dala miliyan 10 na basukan ake bin jirgin shugaban kasa da gwamnatin nan ta gada.

Majiyar na cewa, “Sakamakon jimawar jirgin, kudaden kula da shi na matukar karuwa a ‘yan kwanakin nan, adadin kudaden da ake kashewa wajen kula da jirgin masu matukar yawa ne. Ina mamakin har zuwa yaushe ne za a ci gaba da kashe wannan makudan kudaden wajen kula da jirgin da ya dace a sayar da shi domin sayo sabo fil a leda.”

Babban sakataren kungiyar injiniyoyin da ke kula da jirage da gyarasu (SLAMEN), Sheri Kyari, ya bayar da shawarar a sayo sabon jirgi zai fi kudaden da ake kashewa wajen gyara wannan da ake da shi.

 
People are also reading