Home Back

Napoli ta sanar da ɗukar Conte sabon kociyanta

bbc.com 2024/7/5
Antonio Conte

Asalin hoton, Reuters

Napoli ta naɗa tsohon wanda ya horar da Chelsea da Tottenham, Antonio Conte a matakin sabon kociyanta kan yarjejeniyar kaka uku.

Mai shekara 54, baya jan ragamar wata ƙungiya tun bayan da ya bar Tottenham cikin watan Maris ɗin 2023, bayan wata 16 da ya horar da ita.

Duk da cewar bai taka rawar gani ba a Tottenham, amma ya yi bajintar lashe Premier League a Chelsea a 2016/17 da FA Cup a kaka ta biyu daga baya aka kore shi a 2018.

''Napoli wuri ne mai mahimmaci a duniya. Ina murna da farinciki na ganni a kan bencin ƙungiyar mai launin ruwan bula,''

Conte ya ja ragamar Milan ta lashe Serie A na farko cikin shekara 11 a 2021.

''Zan yi alkawarin cewar, zan yi iya kokarina domin ciyar da ƙungiyar gaba, kuma fatan da yake tare da waɗanda za su taimaka min gudanar da aikin kenan.''

Ɗan kasar Italiya ya ja ragamar Juventus ta lashe Sereie A guda biyu a jere a 2011-2014.

Napoli, wadda ta ɗauki Serie A karon farko a shekara 33 a bara, ta kasa taka rawar gani a bana, wadda ta kare a mataki na tara a teburin babbar gasar tamaula ta Italiya.

Rashin kokarin ƙungiyar ya sa ta katse yarjejeniyar koci, Francesco Calzona, wanda ya kama aiki cikin Fabrairu, bayan korar Walter Mazzarri, wanda ya yi wata uku.

People are also reading