Home Back

JAMB 2024: Hazikin Dalibi Dan Shekara 18 Ya Samu Maki 313 a Jarabawar UTME

legit.ng 2024/5/17
  • Dan shekara 18, Ebeniro Akachi yana kan hanyar cika burinsa na karanta kwas din likitanci da tiyata a jami'ar Fatakwal (UNIPORT)
  • Hazikin dalibin ya samu maki 313 a jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare (UTME) da aka fitar na shekarar 2024
  • Akachi ya yi karatu a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Okigwe kuma ya samu maki 64 a Ingilishi, 84 a Physics, 80 a Biology da 85 a Chemistry

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Bayan samun maki 313 a jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME), dan shekaru 18, Ebeniro Akachi, ya tabbatarwa duniya cewa ana yin nasara idan aka yi aiki tukuru.

Akachi yana son yin karatun likitanci da tiyata a jami'ar UNIPORT
JAMB 2024: Dan shekara 18 ya samu maki 313 a jarabawar UTME, zai karaci likitanci. Hoto: Paschal Ebeniro Asali: UGC

Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2024 a ranar Talata, 29 ga watan Afrilu.

UTME: Akachi ya samu maki 313

Akachi ya yi nasarar samun maki 313 daga darusa hudu da ya amsa tambayoyi a kansu a jarabawar da ya zana karo na biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibin, wanda ya kammala karatunsa a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Okigwe a jihar Imo ya ci 248 a jarabawarsa ta farko.

Mahaifinsa, Paschal Ebeniro, ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a yammacin Laraba, 30 ga Afrilu.

Akachi zai yi karatun likitanci

Hazikin dalibin ya ci maki 64 a Ingilishi, 84 a Physics, 80 a Biology da 85 a Chemistry inda ya samu jimillar maki 313 a UTME 2024.

Dan asalin jihar Imo daga karamar hukumar Ihitte Uboma ya nemi yin karatun likitanci da tiyata a jami’ar Fatakwal (UNIPORT) da ke jihar Ribas.

WASSCE: Akachi ya samu kyakkyawan sakamako

Nasarar da Akachi ya samu a jarabawar UTME 2024 ba abin mamaki ba ne saboda yana da makin A a darusa 2, B a darusa 6 da kuma C a darasi 1 a jarabawarsa ta WASSCE ta 2023.

Ya samu makin A a darasin lissafi da kiwon dabbobi, makin B a darasin ilimin jama'a, Ingilishi, Biology, Chemistry da kimiyyar na'ura mai kwakwalwa, kuma ya samu makin C a darasin 'lissafi mai zurfi'.

Mahaifi ya rubutawa yaronsa UTME

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar JAMB ta kama wani mahaifi da ya yi sojan gona domin zanawa yaronsa jarabawar UTME 2024.

Hukumar ta gargadi masu satar amsa ko tunanin zana ma wani jarabawar tare da cewa tana da kayan aikin gano wadanda ke aikata irin wannan laifin.

Asali: Legit.ng

People are also reading