Home Back

Ana zaben shugaban kasa a Mauritaniya

dw.com 6 days ago
Shugaban Moritaniya Mohamed Ould Ghazouani guda daga cikin 'yan takara
Shugaban Moritaniya Mohamed Ould Ghazouani guda daga cikin 'yan takara

Al'umar kasar Mauritaniya na zaben shugaban kasa a yau, inda za su yanke shawarar sake zaben shugaba mai ci Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani ko kuma wani sabon shugaba.

Kimamin wadanda suka kai shekarun zabe mutum miliyan daya da dubu 900 ne aka yi wa rajista, inda za su fidda mutum guda daga cikin 'yan takara bakwai da ke neman shugabancin kasar.

Mauritaniyar da ke shirin fara fitar da arzikin iskar gas, kasa ce da ake wa kallon mafi kwanciyar hankali a yankin Sahelyanki da ke fama da fitintinun kungiyoyin ta'adda.

A shekara ta 2019 ne dai aka zabi Shugaba El Ghazouani, lokacin da ya kasance karo na farko da ake zaben shugaban kasa tun bayan samun 'yanci daga Faransa a 1960.

Ana dai sa ran samun sakamakon zaben ne tsakanin gobe Lahadi zuwa jibi Litinin.

People are also reading