Home Back

Atiku ya ce laifi ne da har Gwamnatin Najeriya ke ƙoƙarin kamfatar kuɗaɗen ‘yan fansho don ta yi ayyukan raya ƙasa da su

premiumtimesng.com 2024/6/18
Ba a taba mummunar zaɓe cike da jagwalgwalo  a Najeriya irin wanda aka yi ranar Asabar ba, zan ƙalubalanci sakamakon a Kotu – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta dakatar da yunƙurin da ta ke yi na kamfatar kuɗaɗen ajiya na ‘yan fansho da ma wasu kuɗaɗen, da nufin wai za ta yi ayyukan raya ƙasa da su.

Atiku ya yi wannan kira ranar Laraba, bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar cewa ta na da niyyar gabzar maƙudan kuɗaɗe daga cikin Asusun Ajiyar ‘Yan Fansho, domin yin ayyukan raya ƙasa da kuɗaɗen.

Baya ga Asusun Ajiyar Kuɗaɗen ‘Yan Fansho, gwamnatin Tinubu na da niyyar kamfatar kuɗaɗe daga Asusun Kuɗaɗen Inshorar Rayuka da jimillar su ya kai Naira tiriliyan 20.

Atiku ya ce, “idan gwamnati ta yi haka, za ta jefa kuɗaɗen ajiyar da ma’aikata suka shafe shekara da shekaru suna tarawa cikin tsomomuwa.

“Kuma idan aka kamfaci kuɗaɗen nan, nan gaba za a jefa ma’aikatan da za su yi ritaya cikin matsanancin halin ƙuncin rayuwa, saboda su na tara kuɗaɗen domin su rufa wa kan su asiri idan sun yi ritaya daga aiki.”

“Wannan wata hanya ce da gwamnati za ta bi ta karya dokar ƙasa, saboda Gwamnatin Tarayya ba ta da halascin da doka ta ba ta iznin kamfatar kuɗaɗen ajiyar ‘yan fansho da irin makamantan su.”

“Musamman, kada Gwamnatin Tarayya ta yi laifin da ya karya doka:”Ba za a iya ɗibar sama da kaso 5% cikin kaso 100% na kuɗaɗen ‘yan fansho a yi ayyukan raya ƙasa da su ba.” Inji Atiku.

Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun ne ya shaida wa manema labarai cewa waɗannan maƙudan kuɗaɗe idan gwamnati ta yi amfani da su, za a samar da gidaje waɗanda za a bayar a farashi
Ai rahusa da za a shafe shekaru 25 ana biya.

Haka Minista Edun ya bayyana bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a ranar Talata, a Abuja.

Ya ce ai su kuɗaɗen ‘yan fansho abu ne da ke ajiye tsawon lokaci. Ministan ya ƙara da cewa dukkan ɓangarori sun amince da wannan tunani da gwamnatin tarayya ta yi.

Dokar Fansho ba ta halasta wa Gwamnatin Tarayya ramcen kuɗaɗen ajiyar ‘yan fansho don ta yi aiki ko wani abu da kuɗaɗen ba.

Cikin Oktoba sai da Majalisar Tarayya ta zartas da amincewa ta binciki Asusun Ajiyar Kuɗaɗen ‘Yan Fansho, domin ƙwato Naira tiriliyan 10 da aka ce Gwamnatin Najeriya ta ramta.

Kuɗaɗen sun kai kashi 65 bisa 100 na adadin jimillar kuɗaɗen fansho.

People are also reading