Home Back

MATSALAR TSARO: Bayan dawowa daga taron Amurka, gwamnonin Arewa sun tattauna matsalolin tsaro a Kaduna

premiumtimesng.com 2024/5/20
MATSALAR TSARO: Bayan dawowa daga taron Amurka, gwamnonin Arewa sun tattauna matsalolin tsaro a Kaduna

Gwamnonin Arewa sun hallara Kaduna ranar Talata, suka tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin tsaro da ƙara yawaitar yara masu gararamba kan titi da ba su zuwa makaranta.

Wannan ne taron gwamnonin Arewa na farko a 2024, wanda tun taron su na cikin Disamba, 2023 ba su sake hallara a Kaduna ba.

Kamar wannan taron, shi ma na Disamba ɗin matsalar tsaro ce suka fi maida hankali wajen tattaunawa, sai kuma batun ci gaban yankin Arewa.

Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, shi ne ya jagoranci taron.

Sama da shekaru 10 kenan wasu jihohin Arewa na fama da matsalar tsaro, musamman Boko Haram a Arewa maso Gabas, sai kuma mahara da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma. Ga kuma tashe-tashen hankula na faɗan makiyaya da manoma a Arewa ta Tsakiya.

Sannan kuma Arewa na fuskantar matsalar fama da ƙuncin talauci da kuma yawaitar yara masu gararamba kan titina, waɗanda ba su zuwa makaranta.

Gwamnonin sun ƙara jaddada aniyar ƙara himma sosai wajen bunƙasa fannonin ilmi, kiwon lafiya, koyar da sana’o’in hannu, da ayyukan inganta rayuwar jama’a.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin bulaguron Gwamnonin Arewa 10, waɗanda suka rankaya taron sanin-makamar-tsaro a Amurka.

Cibiyar Inganta Ɗorewar Zaman Lafiya ta Afrika da ke Amurka, ta gayyaci Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina da wasu gwamnonin Arewa 9, domin halartar taron zaman lafiya da inganta tsaro a Arewacin Najeriya.

Gwamnonin 10 dai dukkan su su fito ne daga jihohin Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya, wato yankin da kuma ake kira Middle Belt.

CIkin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna na Raɗɗa na Katsina, Ibrahim Kaula ya fitar a ranar Talata, ya ce sauran gwamnonin sun haɗa da Uba Sani na Kaduna, Abba Yusuf na Kano, Nasir Idris na Kebbi, Umar Namadi na Jigawa da kuma Ahmad Aliyu na Sokoto.

Sauran kuma sun haɗa da Dauda Lawal na Zamfara, Hyacinth Alia na Benuwai, Mohammed Bago na Neja, sai kuma Caleb Mitdwang na Filato.

Sanarwar ta ce za su halarci taron na kwanaki uku, wanda za a gudanar a ranakun 23 zuwa 25 ga Afrilu, a Washington, babban birnin Amurka.

Ya ce za ta tattauna matsanancin halin rashin zaman lafiya da tashe-tashen hankunan da ake fama da su a Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya, wato matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

People are also reading