Home Back

HUƊUBAR SHAIƊAN: Kotu ta daure wani manomi da ya yi wa wata tsohuwa mai shekaru 65 fyaɗe

premiumtimesng.com 4 days ago
Prison
Prison

Kotun majistare dake Ado-Ekiti a jihar Ekiti ta daure wani manomi mai shekaru 45 Abajigbin Gbenga a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun Dolamu Babalogbon wanda ya yi watsi da rokon sassauci da Gbenga ya nema ya yanke wannan hukunci ne bayan an same shi da laifin yi wa mata mai shekaru 65 fyade.

Dan sandan da ya shigar da kara Sodiq Adeniyi ya ce Gbenga ya aikata wannan ta’asa a watan Afrilun 2024 a Ipole Iloro- Ekiti.

Adeniyi ya ce matan ta kira Gbenga domin ya yi mata feshi a gonanta.

“ A wannan rana da ya kamata Gbenga ya je ya yi aikin feshin sai ya roki matan ta kawo masa maganin feshin gida ya haɗa daga nan sai su garzaya ginar.

Ko da ta kaeo masa maganin sai ya danneta ya yi lalata da ita.

Babalogbonya ce Gbenga zai zauna a gidan gyara hali har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar.

Za a ci gaba da shari’a ranar 31 ga Yuli.

People are also reading