Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Har Yanzu Tana Biyan Kudin Tallafin Man Fetur

leadership.ng 2024/7/6
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Har Yanzu Tana Biyan Kudin Tallafin Man Fetur 

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen cewae tallafin man fetur zai lakume kimanin Naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024.

Wannan ya saba wa Naira tiriliyan 3.6 da aka biya a kasafin kudin shekarar 2023.

Wani daftarin rahoton shirin Accelerated Stabilization and Advancement Plan (ASAP) wanda ministan kudi, Wale Edun, ya gabatar wa shugaba Tinubu a ranar Talata, ya nuna cewa za a kashe kudaden za a kashe wajen biyan tallafin man fetur a shekarar 2024 ya kai Naira tiriliyan 5.4, inda aka samu karin Naira tiriliyan 1. 8 da aka kashe a 2023.

An gabatar da rahoton ne don magance manyan ƙalubalen da suka shafi yin gyare-gyare da bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

“A halin yanzu, ana hasashen kashe hasashen za a kashe Naira tiriliyan 5.4 a karshen shekarar 2024 a tallafin man fetur.

A baya dai, gwamnatin Tinubu, ta tsaya tsayin daka cewa ba za ta kara biyan kudin tallafin man fetur ba.

A watan Disamba, gwamnatin ta ce sabanin ikirarin da bankin duniya ya yi na cewa gwamnati na ci gaba da biyan tallafin man fetur, ta cire ne don alfanun ‘yan kasar.

Da yake zantawa a gidan talabijin na Channels, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya ce shugaba Tinubu ya bayyana karara tun daga ranar da ya hau mulki cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.

Ministan ya ce cire tallafin ya sanya Nijeriya samun karin kudaden shiga da ke tarawa a asusun tarayya.

A watan Afrilu, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i, ya ce gwamnatin tarayya na kashe kudaden tallafin man fetur fiye da abin da ake biya a baya.

People are also reading