Ana Murnar Dala Ta Karye a Kasuwa, Babban Banki CBN Ya Ɗauki Sababbin Matakai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci halastattun ƴan canji da ke kasuwancin hada-hadar kudi su sabunta lasisin aikinsu.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da dataktan tsare-tsaren kudi na CBN, Haruna Mustafa, ya fitar ranar Laraba, 22 ga wstan Mayu, 2024.
Bankin ya kuma bukaci duk wani ɗan canji ya tabbata ya cika sharuɗɗan nau'in lasisinsa daga nan zuwa watanni shida, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dukkan ƴan canji da masu tallata ƴan kasuwar hada-hadar kuɗi su cike buƙatar neman sabon lasisi na kowane mataki ko nau'in da ya kwanta masu a rai," in ji CBN.
CBN ya yi sabbin sauye-sauye
Har ila yau, babban bankin ƙasar nan ya yi sababbin sauye-sauye a kundin dokoki da ƙa'idojin ayyukan ƴan canjin da aka amince da su.
Ɗaya daga cikin canje-canjen da bankin ya yi shi ne cire tilascin ajiye N200m ga masu lasisi mai dataja ta farko watau Tier-1.
Haka zalika babban bankin ya jingine ajiye N50m ga masu lasisi mai ƙima ta biyu, cewar rahoton Vanguard.
CBN ya kuma janye kudin sabunta lasisi na shekara-shekara na N5m ga ƴan canji da ke matakin fatko da kuma N1m ga ƴan mataki na biyu.
Sanarwan ta ce:
"Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da daftarin ka'idojin gudanar da ayyukan ƴan canji a Najeriya a watan Fabrairun 2024, domin jin ra'ayoyin masu ruwa da tsaki.
"Bayan kamma jin shawarwarin masu ruwa a tsaki, a yanzu CBN ya fitar da daftarin ƙa'idojin da aka amince da su domin sa ido kan ayyuka. ƴan canji a Najeriya."
A wani rahoton kuma
Asali: Legit.ng