Home Back

Kotun Koli Ta Ba Gwamnoni 36 Sabon Umarni Bayan Tinubu Ya Maka Su a Kotu

legit.ng 2024/7/5
  • Yayin da Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 a kotu kan ƙananan hukumomi, Kotun Koli ta ba su sabon umarni
  • Kotun ta bukaci duka gwamnoni 36 da su yi martani kan zarginsu da ake yi game da dakile ƴancin ƙananan hukumomi
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin ta shigar da korafi kan gwamnonin game da ƙananan hukumomi 774 da ke fadin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta ba gwamnonin jihohi 36 wa'adin kwanaki bakwai su yi martani kan kasarsu da aka shigar.

Kotun ta bukaci hakan ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka su a kotu kan ba kananan hukumomi 774 ƴancin kansu.

Har ila yau, kotun ta umarci Ministan Shari'a ya yi martani cikin kwanaki biyu bayan karbar korafi daga gwamnonin, cewar Leadership.

Mai Shari'a, Garba Lawal shi ya ba da wannan umarni bayan korafin Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi.

Karin bayani na tafe....

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

People are also reading