Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 a Zamfara, Fusatattun Matasa Sun Yi Zanga-Zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsafe, jihar Zamfara - Akalla fararen hula 3 ne suka mutu yayin da wasu uku suka samu raunuka a yayin wata arangama tsakanin dakarun Operation Hadarin Daji da ‘yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa harsashi ne ya kuskure ya samu fararen hular a yayin artabun a kauyen Tsafe da ke jihar Zamfara, a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu.
Zagazola Makama ya ruwaito cewa, ‘yan fashin na sanye ne da kayan mata, yayin da wasu kuma suka sanya kayan jami'an tsaro kafin su kai hare-haren a wurare daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar leken asirin ta shaida wa Makama cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wata mota da ke jigilar ‘yan kasuwa zuwa garin Tsafe ta hanyar Gusau zuwa Tsafe.
Haka kuma wasu ayarin 'yan bindigar a kan babura sun shiga kasuwar kauyen tare da bude wuta kan mai uwa da wabi bayan sun bi ta ofishin 'yan sandan garin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar wa da gidan talabijin na Channels kai harin ta wayar tarho.
Ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda harin ya rutsa da su ba amma ya ce an tura jami’an hadin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda zuwa wurin domin fatattakar ‘yan ta’addan.
"Har yanzu ina jiran DPO na Tsafe ya ba da cikakken rahoton halin da ake ciki amma abin da zan iya tabbatar muku a yanzu shi ne sojoji da ‘yan sanda sun awo da zaman lafiya yanzu.”
- A cewar Abubakar.
A hannu daya kuma, Zagola Makama ya ba da rahoton cewa jami’an tsaro sun tarwatsa wasu fusatattun matasa bayan da suka yi zanga-zangar nuna adawa da jami’in ‘yan sandan Tsafe.
Mazauna yankin sun fusata ne saboda jami’an ‘yan sandan ba su yi wani yunkuri na dakile ‘yan bindigar ba a yayin da suka far wa mazauna yankin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta aike da wata tankar yaki mai daukar jami'ai zuwa tsafe domin dakile masu zanga-zangar.
Asali: Legit.ng