Home Back

Ramaphosa ya sha rantsuwar ci gaba da shugabancin Afrika ta Kudu a wa'adi na 2

rfi.fr 2024/7/1
Shugaban Afrika ta  Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa. REUTERS - Nic Bothma

Cyril Ramaphosa ya sha rantsuwar kama aiki don yin wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasar Afrika ta Kudu, bayan da jam’iyyarsa ta ANC ta gaza samun rinjaye a karo na farko cikin shekaru 30, lamarin da ya tilasta mata ƙula haɗaka don kafa gwamnati.

Shugabannin ƙasashen da dama ne suka haalarci wannan bikin rantsawar, cikin su har da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na Angola Joao Lourenco, da na Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso sai kuma sarkin  Eswatini, Sarki Mswati na III.

A jawabin da ya gabaatar  bayan  da ya sha rantsuwar kama aiki, shugaba Ramaphosa ya sha alwashin aiki tukuru don ciyar da ƙasar gaba, kana ya yi kira ga al’ummar ƙasar su ha ɗa kawunansu, su kuma yi watsi da masu ƙoƙarin gwara kawunansu don su yi rikici.

Mafi akasarin ƴan majalisar dokokin ƙasar ne suka zaɓi Ramaphosa mai shekaru 71 a makon da ya gabata, biyo bayan zaɓen 29 ga watan Mmayu, wanda jam’iyyar ANC mai mulkin ƙasar ta gaza samun rinjaye a karon farƙo cikin shekaru 30.

Ana sa ran Ramaphosa ya bayyana sunayen ministocinsa a nan gaba kaɗan, a yayin da ake ci gaba da tattaunawa da abokan haɗaka.

A shekarar 2018 ne Rapmaphosa, tsohon jagoran ƙungiyar ƙwadago ya fara dare karagar mukin Afrika ta Kudu, bayan da wanda ya gabace shi, Jacob Zuma ya yi murabus ala tilas, biyo bayan zarge-zargen rashawa.

People are also reading