Home Back

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a fannin ilimi a jihar

dalafmkano.com 2024/6/25

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a fannin ilimi a jihar, domin samar da tsari da kyakkyawar makoma mai inganci ga al’umma.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da harkar ilimi ke samun koma baya lamarin da gwamnatin jihar ta ɗauki wannan mataki domin ingata fannin.

Da yake ƙaddamar da dokar a fadar gwamnatin jihar Kano, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa harkar ilimi na da matuƙar muhimmanci ga al’umma hakan yasa gwamnatin sa ta ɗauki wannan mataki, domin samar da kyakkyawan tsari a fannin da zai ciyar da jihar Kano gaba.

“Za mu gyara ajujuwan makarantun gwamnati na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar Kano; za kuma mu gina sabbin dakunan ɗaukar karatu a makarantun gwamnati tare da samar musu kujerun zama, “in ji Abba Kabir”.

Gwamnan ya ƙara da cewa bisa la’akari da yadda makarantu Firamare da na Sakandire na jihar Kano suka lalace, ya zama wajibi gwamnatin su ta bai wa ɓangaren ilmin mahimmanci.

Da yake jawabi tun da farko ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, a jam’iyyar NNPP Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya buƙaci gwamnatin jihar Kano, da ta ƙara mayar da hankali wajen inganta harkar ilimi domim samar wa al’ummar jihar kyakkyawar makoma.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, yayin ƙaddamar da dokar taɓaci akan ilmin, gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da bai wa malaman wucin gadi na BEZDA, takardar tabbatar da su a matsayin cikakkun ma’aikatan gwamnati.

People are also reading