Home Back

Tinubu Ya Kinkimo Namijin Aikin da Zai Amfani Mutane Miliyan 30 a Najeriya

legit.ng 2024/6/29
  • Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa mutane akalla miliyan 30 ne za su mori titin Lagos-Calabar ta fuskoki da dama
  • Shugaban wanda ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da titin mai tsawon kilomita 700 ya ce titin zai bunkasa kasuwanci ta hanyar samar da kasuwa
  • Haka kuma Bola Tinubu na ganin gina titin zai bude kofar samar da kayayyakin bukatar yau da kullum da ayyukan yi ga matasa a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana babban titin da gwamnatinsa ke ginawa daga Lagos-zuwa Calabar da alamar ci gaba ce.

Ya ce titin mai tsawon kilomita 700 zai taimaka sosai wajen bunkasa kasuwancin akalla mutane miliyan 30 dake kewaye da titin.

Bola Tinubu
Titin Lagos-Calabar: Shugaban kasa ya ce mutane miliyan 30 za su samu karuwar kasuwanci Hoto: Asiwaju Ahmed Bola Tinubu Asali: Facebook

Punch News ta wallafa Shugaban na cewa haka kuma mazauna yankin za su samu kasuwar sayar da kayan da suke samarwa.Punch News ta wallafa Shugaban na cewa haka kuma mazauna yankin za su samu kasuwar sayar da kayan da suke samarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa za su samu aikin yi,' Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ana sa ran dubbunnan mutane ne za su samu aikin yi kai tsaye yayin gina titin Lagos zuwa Calabar.

Ya bayyana haka ne yayin kaddamar da aikin gina titin a ranar Lahadi a wani bangare na bikin cikarsa shekara guda a kan mulki,kamar yadda Nairaland ta wallafa.

Bola Tinubu ya kara da cewa miliyoyin jama'a ne za su samu wasu ayyukan sanadiyyar ginin titin, ciki har da 'yan siyasa.

Shugaban ya bayyana yakinin cewa aikin zai matso da ci gaba kusa da al'umma, tare da saukaka zirga-zirga.

'Titin Lagos-Calabar: Akwai rashin gaskiya,' Atiku

A baya mun baku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da kin bayyana gaskiya kan kwangilar titin Lagos-Calabar.

Titin mai tsawon kilomita 700 zai ratsa ta cikin jihohin kasar nan tara a hanyarsa ta shiga Calabar daga Lagos, kuma kamfanin Hitech ne ke aikinsa.

Asali: Legit.ng

People are also reading